Zan Yi Murabus Idan Ba A Gurfanar Da Yahaya Bello Ba —Shugaban EFCC

EFCC na zargin Yahaya Bello da biya wa dansa kudin makaranta Dala 720,000 a jajibirin saukarsa daga mulki, alhali lokacin biyan kudin makarantar bai yi ba

Zan Yi Murabus Idan Ba A Gurfanar Da Yahaya Bello Ba —Shugaban EFCC

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede. (Hoto: EFCC)

Shugaban Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Ola Olukoyede, ya sha alwashin yin murabus idan har ba a gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a gaban kuliya ba.

Ola Olukoyede ya yi zargin cewa a jajibirin saukar Yahaya Bello da kujerar gwamna, ya ciri Dala 720,000 daga asusun gwamnati ya biya wa dansa guda ɗaya kudin makaranta, tun kafin lokacin biyan kudin ya yi.

A ganawarsa da ’yan jarida a ofishinsa da ke Abuja, ranar Talata, Olukoyede ya lashi takobin tabbatar da an hukunta duk masu hanu a dakile yunkurin EFCC na kamo Yahaya Bello a makon da ya gabata.

Olukoyede ya ce, “Idan ban  jagoranci kammala binciken da ake yi kan Yahaya Bello ba, zan mika takardar ajiye mukamina na shugaban EFCC.

“Na gurfanar da wasu tsofaffin gwamnoni guda biyu da aka bayar da belinsu a yanzu — Willie Obiano da Abdulfatah Ahmed. Na yi niyyar gayyatar Yahaya Bello tun watan Janairu amma mun tsaya jira umarnin kotu ne.

“Idan zan iya kamo Obiano da Abdulfatah Ahmed da Cif Olu Agunloye, waɗanda suke kamar dangina, me zai hana in kamo Yahaya Bello?”

Olukoyede ya ci gaba da cewa a “A matsayinsa (Yahaya Bell0) na gwamna mai ci, saboda ya san zai tafi, ya ciri Dala 720,000 daga asusun gwamnati ya tura wa wani kamfanin canjin kudi don biyan kudin makarantar dansa guda ɗaya a nan gaba.

“A jiha mai fama da talauci kamar Kogi aka yi haka, kuma kuke so wai in yi shiru, saboda zargin cewa ana amfani da ni?”

A ranar 18 ga Afrilu ne EFCC ta ayyana Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin sa da almundahanar Naira biliyan 80.

Har yanzu dai tsohon gwamnan bai gurfana a gaban kotu ba, duk da irin yaɗa buƙatar gurfanar da shi, tun bayan da aka bayyana cewa ana neman sa.

Shugaban EFCC ya ce ya kira Yahaya Bello ta wayar tarho cikin girmamawa domin ya zo ya amsa tambayoyi kan waɗansu maƙudan kuɗaɗe, amma duka da haka tsohon gwamnan ya ki ya zo a cikin sirri kamar yadda aka bukata.

Amma a nasa bangaren, tsohon gwamnan ya musanta cewa an gayyace shi har ma an kirashi ta wayar tarho.

Masu taimaka masa a ɓangaren kafafen yaɗa labarai ne suka ƙaryata iƙirarin shugaban na EFCC a ranar Talatar.

An dai sha taƙaddama kan kama Yahaya Bello, domin kuwa har kotuna biyu masu daraja iri guda sun ba da hukunci masu cin karo da juna kan kamu da gurfanar da Yahaya Bello a gaban kuliya.

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja

Zulum ya kaddamar da taron gyara karatun tsangaya a Borno