Zanariyar Saminaka ta lashe zaben kujerar Majalisar Dokokin Kaduna

Hukumar INEC, ta bayyana Zinariyar Saminaka, Hajiya Munira Suleiman Tanimu ta jam’iyyar APC, a matsayin wadda ta lashe zaben kujerar Majalisar Dokokin jihar Kaduna, ta Mazabar Lere ta Gabas da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, da aka gudanar a ranar Asabar nan da ta gabata. Zaben Kano: APC tana gaban NNPP da kuri’a […]

Zanariyar Saminaka ta lashe zaben kujerar Majalisar Dokokin Kaduna

Hukumar INEC, ta bayyana Zinariyar Saminaka, Hajiya Munira Suleiman Tanimu ta jam’iyyar APC, a matsayin wadda ta lashe zaben kujerar Majalisar Dokokin jihar Kaduna, ta Mazabar Lere ta Gabas da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, da aka gudanar a ranar Asabar nan da ta gabata.

Zaben Kano: APC tana gaban NNPP da kuri’a 1113

Da yake bayyana sakamakon zaben a garin Saminaka, babban Baturen zaben Farfesa Abdullahi Dalhatu, ya bayyana cewa Manira Suleiman Tanimu ta APC ta sami kuru’a 23,275. A yayin da Garba Emmanuel Bajimai na APGA ya sami kuru’a 1419 sai Muhammad Sunusi Sufwan na LP ya sami kuru’a 7158.
Ibrahim Muktar na NNPP ya sami kuru’a 2137. Sa’idu Hussaini na PDP ya sami kuru’a 22,964. Don haka Munira Suleiman Tanimu  APC ce ta lashe wannan zavb.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu