Zanen alamomin manyan tituna

Ministan Makamashi da Ayyuka da Gidaje Babatunde Raji Fashola ya fi gaban a ce batun sa gaskiya ce tsagwaronta kan cewa matafiya a kan manyan titunan Najeriya suna  shan matukar wahala wajen gane inda suka tunkara saboda hanyoyi ba su da cikakkun zane-zane da alamomi. Ba dadadewa ba ya yi jawabi a wajen taro na […]

Zanen alamomin manyan tituna

Ministan Makamashi da Ayyuka da Gidaje Babatunde Raji Fashola ya fi gaban a ce batun sa gaskiya ce tsagwaronta kan cewa matafiya a kan manyan titunan Najeriya suna  shan matukar wahala wajen gane inda suka tunkara saboda hanyoyi ba su da cikakkun zane-zane da alamomi. Ba dadadewa ba ya yi jawabi a wajen taro na 23 na Majalisar Ayyuka ta kasa, mai taken  “Isassun alamomin hanya: Muhimman turakun inganta manyan tituna da kariya da jin dadi’ wanda ma’aikatarsa ta shirya a Abuja. Fashola ya ce a da kafin a samuwar intanet da bazuwa wayar salular alfarma da masararrafu kasashe da dama sun kikiro taswirarori don taimaka wa ’yan kasarsu da masu harkar suffuri don warware cukurkude-cukurkuden mahadar hanyoyi.

“Amma wadannan nau’ukan taswira kadai ba sa cimma manufa ba tare da alamu han ya ba, wadanda ke yi wa masu amfani da hanya jagora su san nisan  tafiya, ko wane nisan  zango suka ci, yaushe tafiyar za ta kai karshe, kuma mene ne tsawon nisansu daga kauye ko birni da karamar hukuma ko muhiman wurare da suka hada da asibitoci da gidajen mai da otal-otal ko masaukai da za su taimaka wajen saukaka wahalhalun nisan tafiya. Abin takaicin shi ne ko dai wadannan alamomin zane-zane babu su ko sun yi karanci a kan manyan  titunanmu. Saboda haka ka kaddara kana tuka kanka a wani birnin da ba ka taba zuwa ba. Yaya za ka gane mahadar baban titin da ya hade jihohi ko sanin inda za ka sha mai ko wajen kwana in dare ya yi a lokacin tafiya mai nisa, ko samun kula da lafiya idan an yi hadari a kan hanya?

Kamata ya yi ma minista ya fadada abin da yake na gaskiya, inda ya yi batun cewa “muhimman wuraren da suka hada da asibitoci da otal-otal don saukaka wahalhalu.. samun  kula da lafiya idan an samu hadari” saboda wadannan muhimman al’amura babu su kwata-kwata a kan manyan titunan Najeriya. Sai dai wannan kalubale ne ga gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su yadda za su tallafa wajen samar da wadannan abubuwa. Muhimmin al’amari na hakika game da wannan sako shi ne akwai matukar bukatar samar da alamomi da zane-zane a kan manyan titunanmu. Baya ga wadannan al’amura da aka bijiro da su, wani muhimmin abin shi ne rashin alamar karkatar da akalar hanya ko juyawa lokacin aikin ginin hanya ko gyaranta, al’amuran da ke haifar da rudani da wahalhalu da hadurra. Mutum zai iya yin tafiya a kan hanya bayan kwanaki kadan yana tuki kwatsam sai ya ga an toshe hanyar an kakaba mata alamar karkatar da akalar tafiya, amma babu wata alamar gargadi. Wannan al’amari ne da aka fi sabawa da shi. ’Yan fashi a manyan tituna sukan fake da wannan nakasun wajen kai farmaki ga matafiyan da ba su da masaniya.

Yawan aukuwar wadannan al’amura na nuni da nakasu a hukumomin gwamnatin Najeriya, inda ake da dokoki da tsare-tsare da ka’idoji a takarda kawai, amma an fi keta dokoki maimakon dabbaka su. Don haka Giwar Ma’aikatar Fashola ta Makamashi da Ayyuka da Gidaje abin zargi ce wajen nuna ko-in-kula game da alamomin hanya. Muna kira ga minista Fashola ya tabbatar da cewa babu titin da za a bari ba shi da cikakkun alamomi ba. Don  haka ya kamata ya yi abin  da ya dace yadda ginin zai tafi kafada-da-kafada da zane-zanen alamomi, saboda ba a saba ganin cewa an bai wa kamfanonin kwangilar hanya, amma sun yi watsi da zane-zanen alamomi saboda babu shi a yarjejeniyar kwangilar. Idan har za su zama daban, to aikin dan kwangilar zane-zanen alamomin hanya ya tafi tare da masu ginin a lokaci guda.

Ya kamata wannan ma’aikata ta samar da rukunin kwararru masu sa’ido kan hanyoyi don tabbatar da ingancinsu da ci gaba da gyaran zane-zanen da suka dusashe sanadiyyar hadurra ko kai-kawon shanu da sauransu.

Titi bai cika ba idan babu alamomin zane-zane . Yan a da matukar amfani tamkar yadda ake auna ingancin na’urorin  sufurin sama. Don haka muna kira ga kwamishinonin  jiha na ayyuka wadanda suka halarci taron Majalisar ayyuka ta kasa su dauki batun minister da muhimmanci, tare da fadada ayyukan a jihohinsu har ma da inganta hanyoyin yankunan karkara. Babu hanyar da take a Najeriya da za a ce ta karkara ce ko ba ta muhimmanci shi ya sa ba za a yi mata zane-zane da alamomi ba.