Zanga-zanga: An jibge jami’an tsaro a hanyar gidan gwamntin Gombe

Fargabar ɓarkewar zanga-zanga ta sa aka jibge jami’an tsaro a hanyar gidan gwamnatin jihar.

Zanga-zanga: An jibge jami’an tsaro a hanyar gidan gwamntin Gombe

‘Yan Sanda

A ranar Talata 1 ga Watan Oktoba 2024 da Nijeriya take cika shekara 64 da samun ’yancin kai Jihar Gombe take cika shekara 28 da samuwa.

Fargabar ɓarkewar zanga-zanga ta sa aka jibge jami’an tsaro a hanyar gidan gwamnatin jihar.

Wakilinmu ya yi nazarin yadda lamarin tsaro yake inda ya ga an jibge ’yan sanda da jami’an sibil difens da sauransu.

Wasu mazauna garin da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa a hasashensu shi ne babu abin da zai faru domin kowa na harkokin gabansa

Malam Umar Mai Sigari, ya ce jibge jami’an tsaron shi ke nuna cewa wani abu zai faru amma halin da ake ciki ba a sa ran za a samu hayaniya.

Masu shaguna da masu sana’o’i a bakin titi kowa na harkokinsa ba tare da jin tsoro ba.

Jami’an tsaron da wakilinmu ya gani suna zaune ne kawai suna hirarsu domin babu wata alama ta cewa za a yi tashin hankali.

Zaman dar-dar din da ake ciki ya hana gudanar da bikin murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai duk da cewa ’yan sanda sun share kwanaki suna atisayen fareti domin wannan ranar.

A daren Litinin ne wasu kungiyoyin matasa karkashin Kwamred Garba Muhammad Ubale, shugaban kungiyar PCRC da hadin gwiwar CNG da kungiyar dalibai suka gudanar da taron manema labarai suka tsame kansu daga shiga zanga-zangar.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja