Zanga-Zanga: An kama mutum 10 masu ɗaga tutocin Rasha a Gombe

Adadin masu zanga-zanga da suke hannunmu yanzu ya karu zuwa 111, a cewar rundunar ‘yan sandan.

Zanga-Zanga: An kama mutum 10 masu ɗaga tutocin Rasha a Gombe

Rundunar ’yan sandan Gombe ta kama mutane 10 da take zarginsu da ɗaga tutocin kasar Rasha yayin gudanar da zanga zangar tsadar rayuwa a jihar

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan, ASP Buhari Abdullahi ne ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar, Hayatu Usman.

Ya ce an kama mutanen ne da wasu mutum 101 da ake zarginsu da fasa ofishoshin gwamnti da wawushe kayan jama’a a lokacin zanga zangar.

A cewarsa wannan aiki na masu zanga-zangar cin mutunci kasa ne da kuma cin amanar kasa da sauran laifuka masu dangantaka da haka.

“A ranar Litinin, an tayar da hankali da ɗaga tutar wata kasa [Rasha] da wasu masu zanga-zanga suka yi wanda hakan ya saba wa doka,” inji shi.

Ya ce adadin masu zanga-zanga da suke hannunsu yanzu ya karu zuwa 111.

A cewarsa, mutane 9 an tsare su ne saboda shiga cikin zanga-zanga da tashin hankali da kuma kai wa ’yan sanda hari.

Haka kuma ya ce mutum 92 daga cikin ababen zargin sun kasance cikin wadanda ake zargin lalatawa da satar dukiyoyi na gwamnati da na masu zaman kansu.

Ya ci gaba da cewa har yanzu babu rahoton asarar rai tun da aka fara zanga-zangar a jihar.

Ya shawarci al’umma da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, yana mai tabbatar musu da himmar hukumar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin su.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS