Zanga-Zanga: An tsananta matakan tsaro a iyakokin Nijeriya

An ƙirƙiri wani maudu’i game da zanga-zangar wanda aka kira da #EndBadGovernance.

Zanga-Zanga: An tsananta matakan tsaro a iyakokin Nijeriya

Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta bayar da umarnin tsananta matakan tsaro a dukkanin iyakokin ƙasar gabanin zanga-zangar ƙasa da ake shirin gudanarwa.

Shugabar hukumar, Kemi Nanna Nandap ta bayar da umarnin ga dukkan manyan jami’an hukumar masu kula shiyya, da na jihohi da kuma na ƙananan yankuna.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar shige da ficen, DCI Kenneth Udo ya fitar da ymmacin ranar Asabar.

Sanarwar ta ce “Shugabar hukumar shige da fice ta ƙasa ta umarci dukkan kwamandojinmu a kowanne mataki, su tashi tsaye wajen tabbatar da tsaro a bakin aikin su kafin zanga-zangar gama gari da wasu ’yan Najeriya ke shirin yi.’’

Ya ƙara da cewa “Shugabar hukumar ta kuma umarci kwamandojinmu masu kula da kan iyakokin Najeriya su tsaurara bincike domin hana baƙin haure shiga cikin ƙasar domin aikata laifi, musamman a lokacin zanga-zangar.’

NIS ta kuma hori jami’anta su gudanar da aikin su cikin ƙwarewa da gaskiya da kuma riƙon amana a kodayaushe.

Aminiya ta ruwaito cewa masu barazanar zanga-zangar dai sun ce za su fita titunan Nijeriya a ranar ɗaya ga watan Agustan 2024, domin bayyana rashin jin dadin su a kan matsalar tsadar rayuwa da rashin shugabanci nagari.

Sun ƙirƙiri wani maudu’i a kafafen zada zumunta a game da zanga-zangar tasu, wanda suka kira da #EndBadGovernance.

Tun kafin matakin da hukumar shige da ficen ta ɗauka, sauran hukumomin tsaron ƙasar sun yi gargaɗi game da zanga-zangar da kuma abubuwan da za su iya biyo bayan ta.

Daga cikin su akwai hukumar tsaro ta DSS wadda ta ce manufar masu zanga-zanga ita ce “kifar da gwamnati” kuma a cikin wata sanarwa ta ce duk da cewa ta gano masu kitsa zanga-zangar da masu ba su kuɗaɗe amma hukumar tana bin hanyoyin da doka ta tanada waɗanda ba na amfani da ƙarfi ba domin daƙile zanga-zangar.

Sai dai masu shirin zanga-zangar, wadda aka tsara gudanarwa daga ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, sun kafe kai-da-fata cewa sai sun yi zanga-zangar domin nuna wa gwamnati matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar sakamakon matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka tun da ta hau kan mulki a 2023.

Sun ƙara da cewa matakan da gwamnati ta ɗauka na cire tallafin fetur da barin kasuwa ta yi halinta kan kuɗin ƙasar wato Naira sun ƙara jefa ta cikin bala’in, abin da ya sa hauhawar farashi ta kai kimanin 34.19.

Shi kansa Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga masu shirin zanga-zangar da su ba shi lokaci domin aiwatar da “kyawawan” manufofinsa, inda kuma ya gana da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnoni da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauransu domin rarrashin masu shirin zanga-zangar.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki