Zanga-zanga: Ana barazanar hallaka Garkuwan Matasan Zamfara

…suna barazanar hallaka matashin idan bai janye zanga-zangar ya goge bidiyoyn da ya yi a baya ba, amma ya ce allambaran 

Zanga-zanga: Ana barazanar hallaka Garkuwan Matasan Zamfara

Wasu da ake zargin jami’an tsaro ne sun kama Garkuwan Matasan Jihar Zamfara saboda shirin zanga-zangar da ke tafe kan tsadar rayuwa a Najeriya.

A wani bidiyo da ya tayar da kura a kafofin intanet, an ga Garkuwan Matasan Zamfara, mai suna Bashir  jami’an tsaro sun sa masa ankwa a hannu suna dukan sa tare da barazanar hallaka shi.

A cikin bidiyon, an ji jami’an tsaron suna tursasa masa suna dukan sa cewa ya janye daga zanga-zangar, amma ya ce allambaran, “gaskiya ba zan janye ba.”

Jami’an tsaron, wadanda ba su bayyana fuskokinsu ba, sun tambaye shi dalilin zanga-zangar, inda ya bayyana musu cewa zaluncin ne dalili.

Matashin ya ci gaba da cewa, “Ni ne Garkuwan Matasan Zamfara domin sun dora alhakins a kaina.”

A yayin da daya daga cikin jami’an ke umartan dayan ya doki matashin sosai, an ji mai dukan na cewa.

Jami’in tsaro: Za ka janye ko ba za ka janye ba?

Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni, ba zan janye ba.

Jami’in tsaro: Mene ne dalilin zanga-zangar?

Bashir: Saboda zaluncin da ake yi mana ya yi yawa.

Jami’i: Wane irin adalci ne gwamnati ba ta yi muku ba?

Bashir: Komai ba a yi mana ba…

Jami’in tsaro: Wallahi za mu ia kashe ka in ba ka jane ba.

Bashir: Sai dai ku kashe ne…

Jami’in tsaron ya ci gaba da ce wa Bashir: Za ka goge bidiyoyin da ka yi ko ba za ka goge ba?

Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni…

Jami’in tsaro: Wane irin adalci ne gwamnati ba ta yi muku ba?

Bashir: Babu abin da gwamnati ta yi mana.

Jami’in tsaro: to ka janye zanga-zangar.

Bashir: Wallahi ban janye ta ba!

Jami’in tsaro: Ba za ka janye ba? Wallahi za ka iya rasa rayuwarka.

Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni, ba zan janye ba.

Jami’in tsaro: Bidiyoyin da ka yi ka yada wa duniya, ka goge bidiyoyin nan?

Bashir: Wallahi ba zan goge gaskiya ba.

Jami’in saro: Za ka iya rasa rayuwarka a kan wannan.

Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni.

Jami’in saro: Wallahi za mu kashe ka!

Bashir: Wallahi ranka dade sai dai a kashe ni.

Daga karshe dai suka cukwikwiye shi suka tafi da shi.

Kawo yanzu dai, hukumomi ba su ce komai game da lamarin ba.