Zanga-zanga ba za ta hana mu rusau a Abuja ba — Wike
Ministan ya ce babu abin da zai yana gwamnati ci gaba da rusau a Abuja.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya jaddada cewa zanga-zanga ba za ta dakatar da ƙoƙarin gwamnati na tsaftace Abuja ba.
A makon da ya gabata ne, Wike ya bai wa hukumomi umarnin yin rusau a wani yanki da ke kan hanyar Lugbe.
- Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa
- Mayakan Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi
Wannan mataki ya jawo fushi a tsakanin wasu mazauna wurin.
Masu zanga-zanga, ƙarƙashin jagorancin ɗan gwagwarmaya Deji Adeyanju, sun soki tawagar masu yin rusau ɗin.
Adeyanju ya bayyana cewa an ƙone gidaje tare da lalata dukiyar miliyoyin Naira.
“Babu dalilin wannan rusau,” in ji Adeyanju.
“Muna roƙon Shugaba Bola Tinubu ya taimaki waɗanda abin ya shafa, waɗanda ke ƙoƙarin yin rayuwa cikin salama.”
A ranar Lahadi ne, ministan tare da manyan jami’an tsaro suka ziyarci yankin da aka yi rusau don ganin halin da ake ciki.
Ya shaida wa mazauna da abin ya shafa cewar gwamnati za ta ci gaba da yin rusau, saboda wajen na barazana ga tsaro.
Ministan ya yi bayanin cewa babu wata gwamnati da za ta lamunci barin haramtaccen waje, musamman wanda ya zama barazana ga tsaro.
Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa babu wata zanga-zanga da za ta hana aikin rusau a Abuja.
Duk da haka, ya gayyaci wasu mutum biyar da aka naɗa a matsayin wakilan mazauna yankin don tattaunawa kan abin da ya kamata gwamnati ta musu.
A baya, mai magana da yawun mazauna yankin, Abba Garu, ya bayyana wa ministan cewa sun shafe shekaru 35 suna zaune a yankin.
Ya ce kimanin mutum 10,000 ne rusau ɗin ta shafa, inda suka rasa gidajensu da kasuwancinsu.
Garu, ya roƙi ministan da ya taimaka musu wajen samar musu da wani wajen zama.