Manyan Hafsoshin tsaro sun shiga taron sirri
Hedikwatar Tsaro ta kira taron sirrin ne kan zanga-zangar da ke gudana
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya kira taron sirri da manyan hafsoshin tsaro kan zanga-zangar tsadar rayuwa da ke gudana a fadin kasar.
Taron sirrin, wanda ake shirin farawa nan gaba kadan, na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke nuna rashin jin dadi tare da kama masu daga batun tutar kasar Rasha a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da suke gudanarwa.
Ana sa ran zaman zai mayar da hankali ne matakan da hukumomin tsaro za su dauka kamar yadda Shugaban Kasa Bola Bola Tinubu ya ba su kan lamarin.
Mahalarta taron a Hedikwatar Tsaro ta Kasa sun hada da shugabannnin hukumoin DSS, NIA, DIA da kuma Shugaban ’yan sanda.
Sauran su ne manyan hafsohin sojin sama da na kasa da kuma na ruwa.
Wani jami’i a Hedikwatar tsaron ya shaida mana cewa shugabannin hukumomi irin su Kwastam, Immigireshan, Sibil Difens da gidajen yari da sauransu na cikin wadanda aka gayyato.
A ranar Lilitin Shugaban Kasa ya soke zaman Majalisar Zartasar ta Kasa, inda ya yi wani zama da Manyan Hafsoshin tare da ba su umarnin daukar mataki kafin tarzomar da ke tare da zanga-zangar ta wuce gona da iri wajen daga tutocin Rasha.
A ranar ce tutocin Rasha a hannun masu zanga-zangar dauke da kwalaye suka karade gari musamman a manyan birane irin su Kano, Kaduna, Katsina suna wake-wake.
Rasha, wadda ke da karfin iko a yankin Gabas na zaman doya da manja da kasashen yamma, wadanda su ne iyayen gidan Najeriya da sauran kasashen Afirka.
Kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da sauransu sun fuskanci juyin mulki a hannun sojoji a baya-bayan nan, inda daga bisani suka kulla kawance da Rasha, suka juya wa tsoffin iyayen gidansu, irinsu Amurka da Faransa baya.
Shugaban tsaron Najeriy, Janar Christopher Musa, ya ce ganawarsu a Abuja, shugaban kasa ya ba su umarnin murkushe masu daga tutocin na Rasha, saboda laifi ne na cin amanar kasa.
Aminiya ta ruwato yadda ’yan sanda suka yi hole mutane akalla 31 da suka kama kan daga tutocin Rasha — cikin wadanda aka kama har wa wani tela da ke dinka tutocin a Kano.