Zanga-zanga: Babu wanda ya rasu a Katsina — ’Yan Sanda

Rundunar ta ce jama’a su yi watsi da labaran ƙarya.

Zanga-zanga: Babu wanda ya rasu a Katsina — ’Yan Sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa a lokacin zanga-zangar yunwa a jihar.

Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina a ranar Asabar.

“Rundunar tana so ta yi bayani kan wani bidiyo na ƙarya da ke yawo a kafofin sada zumunta wanda ke nuna wani jami’in tsaro kwance ba ya motsi, wai an harbe shi har lahira yayin zanga-zanga.

“An yi wa bidiyon kwaskwarima kuma an fitar da shi cikin yanayin da bai kamata. Babu wani abu makamancin haka da ya faru a lokacin zanga-zangar.

“Gaskiyar magana ita ce, jami’in tsaron da aka nuna a bidiyon jami’in NSCDC ne, wanda ya faɗo daga kan motar sintiri saboda wani hatsari da ya faru da motar a wajen zanga-zangar.

“Nan take aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, inda aka yi masa magani aka sallame shi,” in ji Sadiq-Aliyu.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya, inda ya roƙe su su dinga tantance bayanai ta hanyoyin da ‘yan sanda suka amince da su.

“Muna kuma tabbatar wa jama’a da cewa za mu yi aiki da ƙwarewa, kuma za mu ci gaba da aiki tuƙuru don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Katsina,” ya tabbatar.

HOTUNA: Ɗaurin auren ’yar Kwankwaso ya haɗa Atiku, Obasanjo, Kashim Shettima da manyan ’yan siyasa a Kano

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!