Bata-gari sun yi yunkurin wawushe kaya a Kasuwar Dawanau

An girke jami’an tsaro kimanin 800 bayan bata-gari sun nemi kutsawa su sace kayayyakin abinci a Kasuwar Dawanau da ke Kano da sunan zanga-zangar tsadar rayuwa

Bata-gari sun yi yunkurin wawushe kaya a Kasuwar Dawanau

Kayan hatsi

Bata-gari sun yi yunkurin kutsawa su sace kayayyakin abinci a Kasuwar Hatsi ta Kasa da kasa da ke Dawanau a Jihar Kano da sunan zanga-zangar tsadar rayuwa

Hukumar gudanarwar kasuwar ta ce a sakamakon haka tadauki karin jami’an tsaro sama da 800 domin tabbatar da tsaron kasuwar.

Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Dawanau, Alhaji Muntaka Isa, ya ce hadin gwiwar da suka samu daga sojojin da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaron jihar, ya kara inganta tsaro a kasuwar.

Shugaban kungiyar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin cewa matakin zai kare kasuwar yadda ya kamata daga barna da sata.

Ya kara da cewa karin ’yan banga 400 suna aiki tare da jami’an tsaro domin kare kasuwar.

Domin dakile hakan, kasuwar ta dauki karin ’yan banga 400 don tallafa wa jami’an tsaro.

Isa ya ce mahukuntan kasuwar sun dukufa wajen kara tallafa wa jami’an tsaron da aka tura domin dukiyar jama’a daga barna.

Daga nan ya bukaci mazauna yankunan da ke makwabtaka da kasuawr su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanai kan motsin bata-gari.

A cewarsa, an yi hakan ne da nufin tabbatar da tsaron kasuwar, al’ummarta da masu ruwa da tsaki.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS