Zanga-zanga: Gwamnatin Bauchi ta sanya dokar hana fita a Azare
Wannan na zuwa ne bayan da ɓata gari suka fara fasa shagunan mutane a yankin.
Gwamnatin Jihar Bauchi, ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garin Azare da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Katagum a jihar.
Wannan na cikin sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Muhammed Kashim, ya fitar da yammacin ranar Litinin.
- Masu zanga-zanga da tutar Rasha sun fasa banki a Kaduna
- Tinubu na ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock
Ya ce an sanya dokar ne saboda taɓarɓarewar tsaro a garin Azare da ta kai ga lalata dukiyoyin al’umma.
A cewarsa Gwamnan Jihar, Bala Abdulkadir Mohammed, ya amince da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a ƙaramar hukumar Katagum, nan take, domin shawo kan lamarin.
Gwamnan, ya kuma umarci hukumomin tsaro da su shiga cikin lamarin tare da tabbatar da kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su zama masu bin doka da oda, sannan su bai wa jami’an tsaro haɗin kai a wannan mawuyacin lokaci.
Wannan na zuwa ne, biyo zanga-zangar da matasa a jihar suka fito kan tattalin arziƙi.
Garin Azare da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Katagum, shi ne birni na biyu mafi girma da yawan Jama’a a Jihar Bauchi, bayan babban birnin Bauchi.
Ko da yake ɓarnar da aka yi ta fi muni a Azare domin masu zanga-zangar da kuma ɓata gari sun fasa gidajen manyan ‘yan siyasa da kuma masaukin baƙin gwamnati da kuma wani sashe n sakatariyar ƙaramar hukumar Azare.
Mutanen Azare sun yi zargin cewa masu zanga zangar sun fasa gidan wani tsohon mataimakin gwamnan jihar, tare sa kwashe kujeru da naurar sanyaya ɗaki da wasu kayayyaki.
Har wa yau, ɓata garin sun ƙone ofisoshi da motoci a sakatariyar ƙaramar hukumar Katagum.
Sai dai a gefe guda, mazauna Azare sun yi zargin cewa jami’an tsaro, sun harbe mutum ɗaya daga cikin masu zanga-zangar har lahira.
A garin Bauchi kuwa, matasa sun fito ne daga unguwar Bakaro ɗauke da tutocin ƙasar Rasha.
Amma jami’an tsaro sun tarwatsa su, sannan an girke motocin jami’an tsaro a shatale-talen hanyar da ke kusa da CBN da kuma gidan gwamnatin jihar.
Ko da yake hangi gungun matasan sun shiga babbar kasuwar Muda Lawal ɗauke da gora a hannayensu.
Hakan ta sanya ’yan kasuwar rufe shagunansu don gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ya ci tura domin ba ya ɗaukar waya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.