Zanga-zanga: Gwamnatin Kaduna za ta tallafa wa yaran da aka saki

Gwamnatin ta ce ta ɗauki bayanan yaran ta yadda za ta ke bibiyar rayuwarsu.

Zanga-zanga: Gwamnatin Kaduna za ta tallafa wa yaran da aka saki

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alƙawarin tallafa wa yaran da aka kama bayan zanga-zangar yunwa, domin sauya halayensu zuwa mutane na gari.

Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Dokta Abdulkadir Muazu Meyere ne, ya shaida wa manema labarai bayan sakin yaran.

“Gwamna ya yi alƙawarin cewa wasu daga cikinsu za su samu jari don fara kasuwanci,” in ji shi.

Hakazalika, Meyere ya bayyana cewa gwamnatin za ta sanya ido sosai kan yaran 39 don tabbatar da cewa sun samu kyawawan halaye kafin ba su tallafin.

Gwamnatin ta tattara bayanan yaran, ciki har da adireshinsu da lambobin wayarsu da sunayen iyayensu, domin bibiyarsu.

An kuma yi musu gwaje-gwajen lafiya tare da ba su shawara kan muhimmancin zama mutane na gari.

Shugabannin addinin Musulunci da na Kiristanci sun yi musu wa’azi kan bin koyarwar addininsu da gujewa aikata mugayen halaye.

“Gwamna ya bai wa kowa a cikinsu kyautar Naira 100,000 a matsayin alheri,” in ji shi.

Sakataren ya ce tuni aka miƙa su gidajensu, bayan sallamarsu.

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur