Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina ta kira taron gaggawa

Taron ya gayyato kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsakin da suka hada har da jami’an tsaro.

Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina ta kira taron gaggawa

Gwamnatin Katsina ta kira taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa a kan batun zanga-zangar gama-gari da ake shirin gudanarwa a fadin Najeriya.

Taron wandan mukaddashin Gwamna kuma Mataimakin Gwamna, Faruk Jobe ya kira, na da nufin samo wata hanya domin daukar matakin bai-daya don ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Taron ya gayyato kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsakin da suka hada har da jami’an tsaro.

A ranar Alhamis, 1 ga watan zanga-zanga ne ake sa ran fara zanga-zangar gama gari ta kwana 10 kan tsadar rayuwa a fadin Najeriya.

Akwai qarin bayani nan gaba>>>