Zanga-Zanga: Kungiyar Furofesoshi Kiristoci a Arewa ta yi Allah wadai
Matasa su mayar da hankali kan gudummawar da za su bayar domin gina kasa.
Kungiyar Furofesoshi Kiristoci na Arewacin Najeriya, wato Northern Nigeria Christian Professors Forum (NNCPF), ta ce tana Allah wadai da matasan yankin da na kasa baki daya masu shirin fita zanga-zangar matsin rayuwa da ake shirin gudanarwa.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar ta NNCPF, Farfesa Katuka Yaki ya fitar a Kafanchan, Hedkwatar Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna a ranar Lahadi.
- Janyewar Biden: Amurka ta buɗe sabon babi kan zaɓe
- Doka ta halasta wa ’yan ƙasa fita zanga-zanga — Peter Obi
Farfesa Yaki ya jaddada kira ga matasa da su mayar da hankali kan gudummawar da za su bayar domin gina kasa maimakon ayyukan barna da ka iya lalata makomarsu.
Ya yi kira ga masu shirya zanga-zangar da su yi wa gwamnatin yanzu adalci wajen auna kwazonta, yana mai cewa matsalolin tattalin arziki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke fuskanta gadarsu ya yi.
Farfesan ya bayyana cewa zanga-zanga tana da alaka da siyasa da kabilanci, kuma tana da tasirin karkatar da hankalin shugaban kasa a maimakon ba shi damar bude kofar tattaunawa domin magance matsalolin da kasar ke fuskanta.
Ya yi kira ga masu ingiza matasan kan fita zanga-zanga da su ba da shawarar hanyoyin kawo karshen ’yan fashi da ’yan bindiga da kuma magance matsalolin da suka shafi samar da abinci a Arewacin Nijeriya.
Ya yi kashedi kan amfani da zanga-zanga a matsayin wata hanya ta kawo sauyi, inda yake kira ga matasan da su shiga tattaunawa da jami’an gwamnatin tarayya da na jihohi maimakon zanga-zanga.
Farfesan ya kuma yi kira ga gwamnati ta bai wa matasa tallafi tare da tafiya da kowa wajen yaki da cin hanci da rashawa da kawar da nuna bambanci da wariya.