Zanga-zanga: Majalisar Koli Ta Shari’ar Musulunci Ta Gargadi Matasa
Majalisar Koli Ta Shari’ar Musulunci Ta Gargadi Matasa Kan Zanga-Zanga
Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta yi kira ga matasa da su nisanci zanga-zanga da ake shirin gudanarwa a fadin kasar.
Shehu Muhammad Makarfi, wanda ya wakilci majalisar, a wajen taron bita na kwanaki biyu da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya a Gombe, mai taken “Dogaro da Kai da Kame Kai: Mafi Girman Dabara ga Malamai a cikin Da’awa,” ne ya sanar da haka.
Makarfi ya bayyana cewa duk wanda ke karfafa wa matasan Najeriya su yi zanga-zanga, ba ya yin aiki da maslaha ga kasa.
“Zanga-zanga koma-baya ce ga Najeriya, musamman a Arewacin inda muke jin dadin zaman lafiya.
- DAGA LARABA: Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama
- Sheikh Tijjani Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗi da kayan abinci
“Ba za mu bari bata-gari su tarwatsa zaman lafiyarmu ba,” ya jaddada.
Ya yi kira ga Gwamnan Jihar Gombe, a matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, da ya dauki matakai don hada malamai da sarakuna wajen karfafa zaman lafiya da yi wa jama’a gargadi kan hadarin zanga-zanga.
Makarfi ya yi gargadin cewa wasu matasa na iya amfani da damar wajen aikata abubuwan barna.
Ya ba da misalai na abubuwan da suka faru a baya inda matasa suka kwace kadarori da wayoyin hannu.
A madadin Majalisar Kolin Shari’a, Makarfi ya yi kira ga gwamnati da ta hana zanga-zangar tare da samar da hanyoyin samun abin dogaro don rage wahalar da jama’a ke fama.
Ya kuma ba da shawarar kafa ofishin hadin gwiwa na harkokin addini don saukaka sadarwa tsakanin gwamnati da Majalisar Kolin Shari’a ta Kasa.
A cewarsa, hakan zai ba da damar rijistar makarantu da masallatai, da kuma tsarin daidaiton harkokin addini.
Sheik Sani Yahaya Jingir, shugaban Jama’atu Izalatu Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), wanda Sheikh Hamza Adamu ya wakilta, ya bayyana cewa ba za su goyi bayan zanga-zangar ba, yana ba da misalai na kasashe kamar Libiya da Sudan, inda zanga-zanga ta haifar da rashin tsaro da rikici.