Zanga-zanga: Matasa da Jami’an tsaro sun yi sa-in-sa a Neja

Bayan ’yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su, daga bisani matasan sun sake taruwa suna neman sake rufe hanyar.

Zanga-zanga: Matasa da Jami’an tsaro sun yi sa-in-sa a Neja

’Yan sanda sun yi harbe-harbe bayan matasa sun yi fito-na-fito da su a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a safiyar Alhamis a Jihar Neja.

Jami’an tsaro sun ɗauki matakin ne bayan matasan sun yi yunkurin toshe hanya a yankin Tunga da ke garin Minna.

Bayan ’yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su, daga bisani matasan sun sake taruwa suna neman sake rufe hanyar.

A lokacin da wakinmu ya isa wurin da misalin karfe 9 na safe, ya iske ’yan sanda da ’yan banga suna kokari janye duwatsun da matasan suka tare hanya.

A lokacin kuma masu zanga-zangar da ’yan kallo suna guje-guje bayan iska ta turnuke da hayakin da jami’an tsaron suka harba.

An kuma girke jami’an tsaro iri-iri a wurare daban-daban da ake zargin yiwuwar samun barazanar tsaro.

Daga cikin wuraren har da shataletalen Kpakungu da ke kan hanyar Minna-Bida, ind a baya aka yi irin wannan zanga-zanga.

Masu shaguna da kasuwanni sun kasance a rufe domin guje wa harin bata-gari.

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza