Zanga-zanga: Mutum 2 sun mutu a arangamar ’yan daba da jami’an tsaro a Kano
Zanga-zanga ta rikiɗe zuwa tashin hankali a jihar.
Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Kano, sun nuna mutum biyu sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da ’yan daba da jami’an tsaro suka yi arangama a jihar.
Rikicin ya faru ne a yankin Kunya Chemist kusa da Kurnar Asabe a ƙaramar hukumar Fagge.
- An ƙaddamar da dashen bishiyoyi 200,000 a Dambatta
- Ɗan Sanusi II ya auri ’yar babban ɗan siyasa a Arewa
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan daban sun yi amfani da zanga-zangar wajen fasa shagunan mutane, ciki har da shagon Rufaida Yoghourt.
Jami’an tsaro sun tarwatsa ’yan daban, wanda ya sa suka fara jifan su da duwatsu.
Rahotanni sun ce wani jami’in ɗan sanda a yankin ya jikatta a yayin arangamar, duk da cewa babu tabbas kan faruwar lamarin.
An tura ‘yan sanda yankin, inda suka kafa shingen bincike don daƙile zirga-zirgar mutane a yankin.
Yankin Kurnar Asabe na kusa da barikin sojoji na Bukavu a Kano.
Majiyar ta bayyana cewar waɗanda aka harba da bindiga ma karbar magani a Asibitin Salamatu da ke yankin.
Jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci turo domin lambar wayarsa ba ta tafiya.
Gwamnatin Jihar Kano, ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24, bayan zanga-zanga kan matsin rayuwa ta rikiɗe zuwa tashin hankali a ranar Alhamis, wanda ya ga lalata dukiyar gwamnati da ta ɗaiɗaikun mutane a jihar.