Zanga-Zanga: Jerin bukatun ’yan Najeriya da NLC ta damka wa majalisa

Bukatun NLC sun hada da wgyara matatun man gwamnati da ba wa manoma tallafi da kula da walwalar ma’aikata

Zanga-Zanga: Jerin bukatun ’yan Najeriya da NLC ta damka wa majalisa

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya damka wa mijalisar dokoki ta kasa kundin bukatun al’ummar Najeriya zuwa ga gwamnatin tarayya.

Bukatun da Ajaero ya damka a hannun shugaban Kwamitin Kwadago da Samar da Ayyuka na Majalisar Dattawa, Sanata Diket Plang, sun hada da aiwatar da daukacin bukatun kungiyar kan jin dadin ma’aikata da kuma samar da ayyukan yi ga ’yan kasa.

Sauran su ne, gyara matatun man gwamnati guda hudu da ke kasar da kuma ba wa manoma tallafin noma ba tare da bata lokaci ba, domin saukaka samar a abinci a kasa.

Kwamred Ajaero ya shaida wa Sanata Diket Plang ranar Talatar cewa al’ummar Najeriya sun ganadanar da zanga-zangar lumanar ce saboda yunwar da ke addabar su, inda ya kwatanta halin da kasar ta tsinci kanta da na kasar Zimbabwe.

Shugaban na NLC ya ce zanga-zangar za ta fargar da gwamnati wajen hanzarta yin abin da ya kamata domin shawo kan matsalolin da ke ci wa kasar tuwo kwarya.

A cewarsa, bangarensu da na gwamnati sun riga sun fara tattaunawa kan batun mafi karancin albashi, amma ba su kai ga cim-ma matsaya ba.

A nasa bangaren, Sanata Plang ya ba su tabbacin tattauna bukatun masu zanga-zangar da nufin ganin an yi abin da ya dace.