Zanga-zanga: Ohaneze ta umarci al’ummar Igbo su kaurace

Kungiyar Ohaneze ta ce ’yan kabilar Igbo sun fi kowa yin asara a duk lokacin da aka yi zanga-zanga a fadin Najeriya

Zanga-zanga: Ohaneze ta umarci al’ummar Igbo su kaurace

Uwar kungiyar ’yan kabilar Igbo, Ohaneze Ndigbo, ta umarci ’yan kabilar a fadin Najeriya su kaurace wa zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake shirin yi a watan Agusta.

Wata sanarwa da Mazi Okechukwu Isiguzoro ya fitar a ranar Talata ta ce kungiyar Ohaneze Ndigbo ta gargadi masu zanga-zangar.

Ya bayyana cewa a tsawon tarihi, ’yan kabilar Igbo ’yan kabilar Igbo ne suka fi shan wahala bayan duk wata gagarumar zanga-zanga a fadin Najeriya inda suke asarar rayuka da dukiyoyinsu a fadin kasar.

Sanarwar ta ce, “Na farko dai, kalubalen tsaro da ake fama da shi a yankin Kudu maso Gabas zai hana gudanar da zanga-zanga a cikin aminci.

“Saboda haka, duk wata zanga-zanga da aka shirya yi a yankin Kudu maso Gabas an soke ta, kuma Igbo ba za su shiga ba.”

Isiguzoro ya kara da cewa zanga-zangar za ta kara ta’azzara matsalolin tsaro da ake fama da su a yankin Kudu maso Gabas.

Sannan za ta ba da dama ga masu aikata laifuka da makiyan al’ummar Igbo su yi amfani da zanga-zangar wajen haifar da rudani.

“Na biyu, yiwuwar a sake yin asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar Igbo a zanga-zangar da ke tafe a fadin kasar nan abin damuwa ne.

“A dangane da haka, Ohaneze Ndigbo na kira ga ’yan kabilar Igbo mazauna jihohin Arewa 19 da kuma yankin Kudu maso Yammacin kasar da su kaurace wa zanga-zangar da ta kunno kai domin kare lafiyarsu.”