Zanga-Zanga saboda tsadar rayuwa ba mafita ba ce — Sarkin Musulmi

Mu ɗaura ɗamara wajen gudanar da addu’o’i don ganin Allah Ya sawwaka mana matsalolin da muke fuskanta.

Zanga-Zanga saboda tsadar rayuwa ba mafita ba ce — Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar. (Hoto: Fadar Sarkin Musulmi)

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga jama’ar Najeriya da su guji gudanar da zanga-zanga domin ba ita ba ce mafita kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa a ƙasar.

Kalaman Sarkin Musulmi na zuwa ne yayin jawaban da ya gabatar a fadar gwamnatin Jihar Sakkwato yayin wani taron tattaunawa kan halin da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta.

Yayin taron da aka gudanar a wannan makon, Sarkin ya ce tattaunawa kan abin da suka shafe al’umma abu ne mai kyau “domin duk inda mutane suke akwai albarka kasancewarmu ’yan uwan juna.

“Mun sani cewa babu abin da ya buwayi Allah, saboda haka ya kamata a koma a rika addu’a don neman taimakonSa.

“Mu a nan Sakkwwato damuwarmu duk da matsala ta shafi ko’ina a Nijeriya, shi ya sanya muka haɗu domin ganin yadda za a shawo kan matsalar.

“Akwai buƙatar gwamnati ta yi tunani mai kyau don wasu ba haka suke ba suna fita suna gudanar da zanga-zanga wanda hakan ba shi ne mafita ba.

“Dole a taru a gaya wa juna gaskiya shi ne zai fi samar da nasara shugabanni su shawo kan matsalolin da ake ciki.

“Ya kamata mu zauna da shugabannin kungiyoyi mu tattauna su ba mu shawara.

“Kuma bayan zaman neman shawarwari za mu sanar da gwamnati abin da ake ganin ya kamata ta aiwatar don su ne mafita. Gwamnati tana aiki ne domin talaka ba wai talaka ne zai yi wa gwamnati aiki ba.

“Ya zama wajibi a haɗa kai don taimaka wa gwamnati a shawo kan matsalar, musamman rashin tsaro wadda ita ce ta hana mu noma da samun abinci a garuruwanmu .

“Saboda haka a ɗaura ɗamara wajen gudanar da addu’o’i don ganin Allah Ya sawwaka mana matsaloli,” a cewar Sarkin Musulmi.

Kazalika, ya buƙaci shugabanni da a koyaushe a riƙa tunatar da su kan tsoron Allah “domin shugabancin da ya ba mu abin tambaya ne.

“Mun sani cewa gwamnati ta damu da halin da ake ciki kuma da ikon Allah sauki zai samu, saboda haka a ci gaba da haƙuri da yi wa shugabannin addu’a.”