Zanga-zanga ta ɓarke kan kisan Sarkin Gobir
Bayan Azahar ranar Alhamis ne fusatattun matasaba birnin Sakkwato suka fito kan tituna suna kone-kone domin nuna takaicinsu
An yi kone-kone a kan tituna a yayin zanga-zangar nuna adawa da kisan gilla da ’yam bindiga suka yi wa Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Isa Muhammad Bawa a Jihar Sakkwato.
Bayan Azahar ranar Alhamis ne fusatattun matasaba birnin Sakkwato suka fito kan tituna suna kone-kone domin nuna takaicinsu kan kisan basaraken.
Matasan sun yi kone-konen a wasu wuraren gwamnati a garin Sabon Birni sai dai daga bisani jami’an tsaro sun samu nasarar kwantar da tarzomar.
Tarzomar ta tashi ne kimanin sa’o’i uku bayan an gudanar da Sallar Jana’izar Marigayi Sarkin Gobir na Sabon Birni ba tare da gawarsa ba a fadarsa da ke Sabon Birni.
Ranar Laraba da dare ne dai aka tabbatar da mutuwar sarkin bayan da ’yan bindiga suka sako jikansa, Kabiru Isah, wanda suka sace su tare a Jihar Sakkwato.
Duk kokarin wakilinmu na yin magana da Kabiru Isah ya ci tura, domin danginsa sun ce ba yanzu zai yi magana da manema labarai ba, sai likitoci sun tabbatar da lafiyarsa da kwarin jikinsa.
Haka kuma, dangin sun ce ba za su ce komai kan Sarkin Gobir ba a yanzu, amma dai za su yi magana kan mutuwar tasa.
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir sun binne gawarsa ne bayan da suka yi kashe shi, jim kadan da cikar wa’adin da suka bayar na kai musu kuɗin fansa.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Litinin ne ’yan ta’addan suka kashe basaraken.
Kokarin wakilinmu na yin magana da kakakin rundunar ’yan sanda a a Jihar Sakkwato, NAhmad Rufa’i, bai yi nasara ba, domin kuwa wakilinmu yi ta kiran sa amma jami’in bai daga waya ba.