Zanga-zanga ta ɓarke kan wahalar man fetur
Masu zanga-zanga kan wahalar man fetur na neman Tinubu ya sallami shugaban NNPCL, Mele Kyari
Zanga-zanga ta ɓarke a Babban Birnin Tarayya Abuja sakamakon wahalar man fetur da ake fama da ita.
Mazauna Abuja ɗauke da kwalaye sun yi da zanga-zangar wahalar man fetur ne a ranar Litinin, suna neman gwamnati ta gaggauta magance matsalara faɗin Najeriya.
Sun kuma buƙaci a rage farashin man, suna masu bayyana cewa tsadarsa ce ta jefa al’umma cikin mawuyacin hali.
Sun kuma buƙaci Shugaba Tinubu ya sallami Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, saboda matsalar man fetur da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Zanga-zangar ta ɓarke ne washegarin da kamfanin NNPCL ya sanar cewa yawan bashin tallafin mai da dillalan mai suke bin sa na neman kawo cikas ga ƙarfinsa na samar da wadataccen mai a Najeriya.
Kamfanin ya bayyana cewa basukan suna kawo cikas ga harkokinsa, tare da barazana ga samun daidaito wajen samar da man fetur a ƙasar.
Masu zanga-zangar da suka taru a Unity Fountain da ke Abuja sun koka bisa yadda ake fama da matsalar mai a Najeriya, alhali Allah Ya albarkaci ƙasar da ɗanyen mai.
Shugaban masu zanga-zangan, Aminu Abbas, ya ce, “muna kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da duk masu rike da madafun iko cewa yanzu ne lokacin da ya kamata su ɗauki mataki, ku tabbatar mana cewa kuna tare da talakawa ba da azzalumai ba.
“Ya kamata a sallami Kyari daga aiki sannan a yi wa NNPCL garambawul domin kamfanin ya koma yin ayyukan da za su amafni al’ummar Najeriya.’’