Zanga-zanga ta barke a Abuja kan tsige Ndume

Al’ummar Borno ta Kudu sun yi zanga-zanga a Abuja kan tsige Sanatansu, Mohammed Ali Ndume, saboda sukan Gwamnatin Tinubu kan matsin rayuwa

Zanga-zanga ta barke a Abuja kan tsige Ndume

Al’ummar Borno ta Kudu sun yi dafifi a Abuja suna zanga-zangar adawa da tsige Sanatansu, Mohammed Ali Ndume, a matsayin babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa.

An tsige Ndume ne saboda sukar Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayan wata wasika da shugabannin jam’iyyarsa ta APC ta kasa suka aika wa majalisar.

An kuma sauke shiga ga mukamin mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan kasafin kudi.

An maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa) a matsayin babban mai tsawatarwa.

Sai dai masu zanga-zangar a karkashin Kungiyar Cigaban Borno ta Kudu da suka kai taru a Unity Fountain da ke Abuja, sun bukaci shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya mayar da Ndume.

Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zangar Mohammed Ibrahim Biu, ya ce Ndume hazikin Sanata ne wanda ya yi wa al’ummarsa hidima tsawon shekaru kuma ba za a iya hukunta shi ba saboda fadin gaskiya.

Ya ce tsige Ndume daga mukamin babban mai tsawatarwa illa ne ga yankin Borno ta Kudu da ma Najeriya gaba daya, yana mai jaddada cewa dole ne a yi adalci.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe