Zanga-zanga ta barke a Kano kan yunkurin daukar matakin soji a Nijar
Daukar matakin yaki a Nijar rashin adalci ne da Turawan Yamma suka kitsa.
Wasu masu zanga-zanga sun mamaye tituna a Jihar Kano suna bayyana adawa da yunkurin daukar matakin soji kan wadanda suka yi juyin mulki a Jamhuriyyar Nijar.
A kwanan nan ne Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta bai wa dakarunta umarnin zama cikin shirin ko-ta-kwana domin warware tankiyar da ta kunnu a kasar da ke makwabtaka da Najeriya.
- Na rasa mijin da babu kamarsa —Matar Sheikh Albani Kuri
- An dage taron Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS kan matakin soji a Nijar
Aminiya ta ruwaito cewa, masu zanga-zangar dauke da tutocin Najeriya da Nijar sun fito a wannan Asabar suna masu bayyana adawarsu kan shirin tura dakarun Jamhuriyyar Nijar.
A yayin da suke tattaki a Kano, suna yekuwar cewa “al’ummar Nijar ’yan uwanmu ne da an riga an zama daya.
“Da mu da mutanen Nijar babu bambanci, ba ma son yaki.
“Daukar matakin yaki a Nijar rashin adalci ne da Turawan Yamma suka kitsa.”
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kiraye-kiraye da gargadin daukar matakin soji a Nijar, musamman daga Arewacin Najeriya.