Zanga-Zanga ta hana jirage fiye da 100 tashi a Jamus
Masu zanga-zangar sun karya shingen jami’an tsaro tare da kutsa kai kan titunan jirage.
Masu zanga-zangar rajin kare muhalli sun hana fiye da jirage 100 tashi a filin jirgin saman birnin Frankfurt da ke zaman mafi yawan hada-hadar jiragen sama a Jamus.
Dubban masu rajin kare muhallin sun tsara gudanar da zanga-zanga a kasashen Turai baki daya, domin dakile zirga-zirgar jiragen sama a daidai lokacin da mutane da dama ke tafiya hutun bazara da nufin nuna illa da barazanar sauyi ko dumamar yanayi.
- Zanga-Zanga: Tinubu da gwamnonin APC na ganawar sirri
- Hisbah ta haramta wa daliban Kano bikin ‘Candy’
Rahotanni daga filin jiragen saman na Frankfurt sun nuna cewa masu zanga-zangar sun karya shingen jami’an tsaro tare da kutsa kansu kan titunan jiragen saman.
DW ya ruwaito cewa wannan lamari dai ya tilsta ’yan sanda da jami’an kashe gobara da sauran jami’an tsaron filin jiragen saman daukar mataki.
Masu zanga-zangar dai sun tilasta soke tashin kimanin jiragen sama 140, kuma kawo yanzu babu wani karin bayani kan sabon lokacin da aka tsara tashinsu saboda fargabar sake samun kutsen ’yan rajin kare muhallin.