Zanga-zanga ta juye zuwa rikici mafi muni a zamanin Macron

Mutane miliyan 3 da rabi ne suka fito wannan zanga-zanga a fadin Faransa.

Zanga-zanga ta juye zuwa rikici mafi muni a zamanin Macron

Masu zanga-zanga a Faransa sun yi arangama da jami’an tsaro a wani rikici mafi muni a cikin watanni 3 da aka fara nuna rashin amincewa da shirin sake fasalin fansho da shugaba Emmanuel Macron ya bijiro da shi.

Adadin masu zanga-zangar da suka fito a birnin Paris ya zarce na sauran kwanaki, biyo bayan sake fusata al’umma da shugaba Macron ya yi a tattaunawarsa da wata tashar talabijin, inda cikin izza, ya nuna ba-gudu-ba-ja-da baya a kan batun sake fasalin fansho.

Kakkarfar zanga-zangar dai ta barke ne a kokarin kalubalantar garambawul din da Macron ke shirin yi wa dokar fansho, wanda gwamnatin kasar ta dauki aniyar tilasta wa ma’aikata karbar sa ba tare da an kada kuri’a a Majalisar Dokoki ba.

Rikicin dai ya kasance wani tashin hankali da Faransa ta gani a cikin gida mafi muni a wa’adin mulkin shugaba Macron na biyu, bayan wa’adinsa na farko ya gamu da mabanbantan bore ciki har da zanga-zangar masu yaluwar riga ko kuma yellow vest da suka shafe watanni suna gangami.

Mahukuntan Faransa sun ce kusan ‘yan sanda 150 ne suka samu raunuka a arangamarsu da masu zanga-zangar ta ranar Alhamis bayan dubun dubatar masu boren suka zabi rikidewa zuwa rikici a birane daban-daban ciki har da Paris inda aka kunna wuta a tsakiyar birnin.

Wutar da aka kunna a kofar shiga babban dakin taron birnin Bordeaux ta lalata katafariyar kofar shiga, sai dai magajin garin birnin ya ce ‘yan kwana-kwana sun kashe wutar cikin mintuna 15.

Kungiyoyin kwadago sun yi ikirarin cewa mutane miliyan 3 da rabi ne suka fito wannan zanga-zanga a fadin Faransa, a yayin da dubu dari 8 suka fito a babban birnin kasar.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50