Zanga-Zanga: Tinubu da gwamnonin APC na ganawar sirri
An dakatar da zaman Majalisar Zartarwa da aka shirya yi a ranar Alhamis, 25 ga watan Yulin 2024.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da wasu gwamnonin jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Kasar da ke Abuja.
Wannan dai na zuwa ne bayan dakatar da zaman Majalisar Zartarwa ta ƙasa da aka shirya yi a ranar Alhamis, 25 ga watan Yulin 2024.
- Akwai lauje cikin nadi a zanga-zangar da aka shirya —Gamji
- Sojoji sun yi wa masu shirin zanga-zanga kashedi
Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma ne ya jagoranci gwamnonin zuwa ofishin shugaban ƙasa tare da shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Abdulrazaq Abdulrahman na Kwara.
Daga cikin mahalarta taron akwai mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, Gwamna Bassey Otu na Kuros Riba, Gwamna Hyacinth Alia na Benuwe, Gwamna Uba Sani na Kaduna da Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi da sauransu.
Duk da cewa babu tabbaci kan maudu’in taron shugaban ƙasar da gwamnonin, ana zargin cewa ba za ta rasa nasaba da yunƙurin daƙile zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar.
Tun ba yanzu ba dai Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa tana ƙoƙarin ganin ta daƙile zanga-zangar da ake ’yan ƙasa ke shirin yi a ranar 1 ga watan Agusta.
Aminiya ta ruwaito cewa Tinubu ya roƙi ‘yan ƙasar da su janye shirin zanga-zangar da suke niyyar yi a farkon watan Agusta mai kamawa.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris ne ya shaida wa manema labarai hakan a fadar gwamnati a Abuja bayan kammala ganawarsa da shugaban kasar a ranar Talata.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar da su dakatar da ita su jira su ga matakin da zai ɗauka a kan ƙorafe-ƙorafensu.
Roƙon na Shugaba Tinubu na zuwa ne a yayin da ake ta ci gaba da batun gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da ‘EndBadGovernance’, a fadin ƙasar musamman ma a shafukan sada zumunta.