Zanga-zanga: Tinubu ya bayar da umarnin sakin yaran da aka tsare

Tinubu ya ce za a hukunta duk waɗanda ke da hannu wajen kama ƙananan yaran.

Zanga-zanga: Tinubu ya bayar da umarnin sakin yaran da aka tsare

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin sakin ƙananan yaran da aka kama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance.

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin.

Idris, ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya umarci Antoni-Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, da ya tabbatar an saki yaran nan take.

Ya ce, “Shugaban ƙasa ya umarci a saki dukkannin yaran kuma a mayar da su wajen iyayensu duk inda suke a ƙasar nan.

“An kafa wani kwamiti da za duba abubuwan da suka shafi kama su da sakin su. Duk wani jami’in tsaro da aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.”

Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), ta yi kira da a dakatar da tuhumar da ake yi wa yaran.

ACF ta soki shari’ar da ake yi wa yaran, inda ta bayyana ta a matsayin abun kunya.

Shugaban Matasa na ƙungiyar Tijaniyya ta Afirka, Sheikh Ahmed Umar, shi ma ya roƙi Shugaba Tinubu da ya sa baki don sakin yaran nan take.

Ya yi Allah-wadai da matakin gwamnati, insa ya bayyana tuhumar ƙananan yaran da rashin dacewa.

Ya ce an ci zarafin yaran ta hanyar tsare su har na tsawon kwana 90.

Sheikh Umar ya bayyana cewa, “Abin mamaki ne ganin yaro ɗan shekara 10 da ba shi da masaniya game da waɗannan tuhume-tuhume, yana fuskantar irin wannan babban laifi.

“Muna roƙon Shugaba Tinubu da ya saki yaran nan tare da biyansu diyya nan take.”

Umar, wanda ya jagoranci Taron Matasa na Arewa da aka shirya a ƙarƙashin ƙungiyar National Youth Alliance a Kaduna, ya jaddada muhimmancin matasa wajen magance matsalolin ƙasa.

Ya kuma yi kira ga matasan Najeriya da su farka kuma su taka rawa wajen ci gaban ƙasar nan.