Zanga-zanga: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai yi jawabi game da halin da ƙasar nan ke ciki.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu, zai yi wa al’ummar Najeriya jawabi a kafafen watsa labarai a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na safe.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Asabar.
- Zanga-zanga: Mutum 2 sun mutu a arangamar ’yan daba da jami’an tsaro a Kano
- Zanga-zanga: Babu wanda ya rasu a Katsina — ’Yan Sanda
Za a haska jawabin shugaban a kafafen yaɗa labarai daban-daban.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka shiga rana ta uku ta zanga-zangar kawo ƙarshen gurɓataccen shugabanci da kuma yunwa a ƙasar.
Zanga-zangar ta faro ne a ranar Alhamis a faɗin Najeriya.
A wasu jihohin an yi zanga-zangar cikin lumana ba tare da samun tashe-tashen hankula ba.
A jihohin Kano, Yobe, Borno, Jigawa, Katsina da sauransu an samu tashe-tashen hankula, lamarin da ya kai ga lalata kadarorin gwamnati da wawushe dukiyar al’umma.
Tuni aka sanya dokar hana fita a jihohin Kano, Borno da kuma Yobe.
Sai dai da safiyar ranar Asabar, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sassauta dokar hana fita a jihar.
A Jihar Kano, kuwa al’amura na ci gaba da ta’azzara duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya.