Zanga-zanga: ’Yan sanda sun gurfanar da mutane 800, sun tsare 90

Sama da mutane 90 da ake zargi an kama su, ciki har da teloli da suka ɗinka tutoci da masu ɗaukar nauyinsu.

Zanga-zanga: ’Yan sanda sun gurfanar da mutane 800, sun tsare 90

Tutar Rasha

‘Yan sanda sun fara shari’ar mutane 800 da aka kama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a faɗin Najeriya.

Rundunar ta ce adadin mutanen da aka kama da laifin ɗaga tutocin ƙasar Rasha a jihohin Kano da Kaduna da Bauchi da Katsina ya kai 90.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka haɗa kai da ’yan sanda suka kai samame a wasu shagunan ɗinki a Kano da sauran wurare domin kamo masu ɗinka tutocin.

Da farko an kama wani tela da wasu mutane 30 da suke ɗaga tutocin a safiyar ranar Litinin, wanda ’yan sanda suka bayyana da laifin cin amanar ƙasa.

Da yake sanar da sabbin kamen da jami’an suka yi a ranar Talata, kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce jami’an rundunar suna bakin ƙoƙarinsu wajen kama waɗanda suka ɗauki nauyin lamarin.

“Sama da mutane 90 da ake zargi an kama su, ciki har da teloli da suka ɗinka tutoci da masu ɗaukar nauyinsu.

“Ana ci gaba da ƙoƙarin kamo wasu da suka ɗauki nauyin samar da tutoci da kuma rura wutar waɗannan munanan ayyuka.”

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS