Zanga-zangar adawa da gwamnati ta tsananta a Sudan
Daya daga masu boren ya riga mu gidan gaskiya.
Daruruwan ’yan Sudan sun sake fantsama a kan titunan birnin Khartoum don nuna adawa da ci gaba da rike madafun iko da gwamnatin rikon kwarya ta soji ke yi.
A zanga-zangar ta wannan Talata, an yi fito na fito tsakanin masu boren da jami’an kwantar da tarzoma na Sudan, inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare ma da harba albarusai da harsasan roba.
- Jami’an tsaro sun cafke Alhassan Doguwa
- INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zabe duk da zanga-zangar da ta barke a Abuja
DW ya ruwaito cewa daya daga masu boren ya riga mu gidan gaskiya bayan da harsashi ya ratsa kirjinshi.
Kasar ta Sudan ta shiga cikin halin rashin tabbas tun bayan da sojoji suka hambarar da halartaciyar gwamnatin farar hula.
A karshen shekarar da ta gabata ne, shugabannin soji da na farar hula suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rigingimun da suka mamaye Sudan tun bayan kifar da mulkin kasar.