Zanga-zangar EndSARS shiri ne na cin mutuncin Buhari – Rashida Mai Sa’a

Ya kamata matasa su farga a daina amfani dasu wajen tada hankali.

Zanga-zangar EndSARS shiri ne na cin mutuncin Buhari – Rashida Mai Sa’a

Rashida Adamu Abdullahi, daya daga cikin fitattun jarumai mata a  masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, ta ce suna goyon bayan Shugaban kasa Muhamamdu Buhari, domin zangar zangar da ake gudanar wa a yanzu wani shiri ne na cin mutuncin Shugaban kasar.

Jarumar wadda ake yi wa lakabi da Rashida Mai Sa’a, ta wallafa wani hoton bidiyo na tsawon mintuna 6 a shafinta na Instagram, inda ta bayyana cewa ana yi wa shugaba Buhari makarkashiya.

“Wannan zanga-zangar da ake yi akwai wata manufa a cikinta, duba da yadda aka ci gaba da tada hankalin mutane duk da cewa Shugaba Buhari ya soke rundunar ’yan sanda ta SARS”.

“A cikin tafiyar Shugaban Kasa, ’yan Arewa sun fi samun manyan gurabe duk da haka akwai wanda ake amfani da su wajen yi masa zangon-kasa”.

Rashida ta kara da cewa “ya kamata matasa su farga a daina amfani dasu wajen tada hankali, domin akwai wanda ba son ci gaban Najeriya suke ba”.

A cikin bidiyon, Rashida ta bayyana cewa ’yan masana’antar Kannywood ba sa tare da wannan zanga-zangar ta #EndSARS da aka shirya.

A cewarta, duk dan Arewan da yake da kishi, tabbas ba zai goyi bayan zanga-zangar ba.

Ta kara da cewa mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, ta sha yin kiraye-kiraye a baya domin a gyare-gyare a Gwamnatin Shugaban Kasa, amma wasu suka rinka ganin laifinta.

Ta ce “Aisha Buhari tana da gaskiya, domin ta san mutanen da ya kamata a ce an yi tafiyar gwamnati da su, wato wanda suka yi fadi-tashi a tafiyar Shugaba Buhari.

Rashida ta ce in har da gaske gyara ake bukata, kamata ya yi a zauna a teburin sulhu domin duba bukatun kowa ba wai a ringa tada hankalin jama’a ba.

Daga karshe ta ja hankalin Shugaba Buhari, a kan ya farga tare da yin gyara a cikin wanda yake tafiya dasu, inda tace akwai bara-gurbi, kuma dole sai ya sauya wanda suke masa zangon-kasa.

 

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya