Zanga-zangar kungiyar kwadago raini ne —Ministan Shari’a
Ministan Shari’a Lateef Fagbemi ya cewa zanga-zangar da kungiyar kwadago ta NLC da TUC suke shirin gudanarwa raini ne ga bangaren shari’a
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi
Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya bayyana cewa zanga-zangar da kungiyar kwadago ta NLC da TUC suke shirin gudanarwa raina umarnin kotu ne.
Ministan shari’an ya sanar da haka ne a wasikar da ya aike wa lauyan kungiyar kwadagon game da shirin zanga-zangar da za a gudanar ranar talata.
A cewarsa, zanga-zangar ta ta’allaka ne a kan tsadar man fetur da na katan masarufi, jin dadin ma’aikata, da kuma tallafin cire tallafin man fetur da wasu tsare-tsaren gwamnati kuma bangarorin sun kulla yarjejeniyar a kai.
“Ku tuna cewa wadannan batutuwa su ne tushen shari’ar da ke gaban Kotun Masana’antu ta Ƙasa.
- Najeriya ta maida wa Nijar wutar lantarki
- Boko Haram Ta Sake Lalata Turakun Wutar Lantarki Mai Karfin 330KVA A Yobe
“Bayan gabatar da korafe-korafe ga kotu, masu shigar da kara ba su da hurumin yin zanga-zanga a kan batutuwan, saboda yin hakan babban wulakanci da cin fuska ga bangaren shari’a.
“Saboda haka zanga-zangar da ake shirin yi a duk fadin kasar ya saba wa umarnin wucin gadi da kotu ta bayar a 2023 a shari’ar tsakanin Gwamnatin Tarayya da NLC da TUC, inda aka hana su kowane irin zanga-zanga ko shiga yajin aiki,” in ji shi.