Zanga-zangar tsadar rayuwa ta barke a Ibadan
Daruruwan mutane a garin Ibadan sun mamaye tituna a garin Ibadan domin gudanar zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa a fadin Najeriya
Da sanyin safiyar yau Litinin ne daruruwan mutane maza da mata suka fito dauke da rubutattun kwalaye a birnin Ibadan hedikwatar Jihar Oyo suna zanga-zangar lumana domin nuna damuwa kan tsadar rayuwa da ta shafi kasa baki daya.
Wasu daga cikin rubutattun kwalayen na kira da ‘A kawo karshen tashin farashin kayan abinci’, ‘Muna bukatar mulkin soja a yanzu’, ‘A sama mana kayan abinci da kula da lafiyarmu da sauran bukatun yau da kullum’, ‘Mun yi kuskuren zaben shugaban kasa’.
Aminiya ta halarci unguwar Mokola Round-About a birnin na Ibadan inda masu zanga-zangar ke rera wakokin batunci ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ana gudanar da zanga-zangar ta Ibadan ce a gaban ’yan sanda da sauran hukumoin tsaro da suke dauke da bindigogi da sauran kayan aikin ko-ta-kwana.
- Murja: Sheikh Daurawa bai yi murabus ba —Hukumar Hisba
- Yau za a ci gaba da shari’ar Ramlat ’yar TikTok
Aminiya ta gano cewa sanarwar fara wannan zanga-zangar ta fito ne da yammacin Lahadi da aka watsa ta intanet ba tare da sunan mutane ko kungiyar da ta shirya gangamin ba.
Hakan ne ya sa rundunar ’yan sandan Jihar hanzarta girke jami’anta a unguwar ta Mokola Round-About da ke kusa da ofishin gwamna da sakatariyar gwamnati domin guje wa barkewar rikici.