Zanga-zangar tsaye kyam ta karbu a Turkiyya

Wani mai shirya kade-kade da raye-rayen biki, dan Turkiyya, Erdem Gunduz ya bullo da dabarar yin zanga-zanga a tsaye, ba tare da hargowa ba, inda ya tsaya tsaye kyam a dandalin Taksim da ke birnin Istanbul. A halin yanzu, sabon salon zanga-zangar wannan dan wasa ta samu karbuwa a kasar Turkiyya.Duk da cewa Gunduz ba […]

Zanga-zangar tsaye kyam ta karbu a Turkiyya
Zanga-zangar tsaye kyam ta karbu a Turkiyya

Wani mai shirya kade-kade da raye-rayen biki, dan Turkiyya, Erdem Gunduz ya bullo da dabarar yin zanga-zanga a tsaye, ba tare da hargowa ba, inda ya tsaya tsaye kyam a dandalin Taksim da ke birnin Istanbul. A halin yanzu, sabon salon zanga-zangar wannan dan wasa ta samu karbuwa a kasar Turkiyya.
Duk da cewa Gunduz ba ya son kanbama kansa, amma sakonnin twitter da ke nuna goyon baya ga wannan sabon salon zanga-zangar tsayue kyam da ya bullo da ita. Kuma ana ta baza hotunsa, inda ya yi tsaye kyam a dandalin Taksim, ya yi shiru ba tare d ahargowa ba.
A wata hira da gidan talabijin Hurriyet ya yi da Erdem Gunduz, ya ce “ta yiwu kafafen yada labarai da al’umma su koyi wani abu daga salon tsaye kyam ba tare da cewa uffan ba.” Sannan ya ce: “Ta yiwu su tausaya. Ni dai mutum ne dan kasa irin kowa. Muna so ne a fahimci manufarmu.”
Gunduz dai ya tsaya tsaye kyam yana fuskantar Cibiyar Yada Al’adu ta Ataturk, wadda aka daura mata tutar Turkiyya da butuntumin jigo juyin juya halin Turkiyya, Mustafa Kemal Ataturk. Saboda ba su fahimci manufar Gunduz ba, sun dauka yana da wata manufa ta addini, al’amarin da ya karya nan take.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda