Zanga-zangar zawarawa a Zamfara: Gwamna ya nemi masu hali su kara aure
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ya yi kira ga masu hali su kara aure domin rage zawarawan da ke jihar sakamakon halin da suke ciki.Gwamna Abdul’aziz Yari ya yi wannan kira ne a lokacin da yake nasiha a wa’azin da ake gabatarwa mako-mako a jihar, inda ya ce ya dace kwamishinoni da masu […]

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ya yi kira ga masu hali su kara aure domin rage zawarawan da ke jihar sakamakon halin da suke ciki.
Gwamna Abdul’aziz Yari ya yi wannan kira ne a lokacin da yake nasiha a wa’azin da ake gabatarwa mako-mako a jihar, inda ya ce ya dace kwamishinoni da masu ba da shawara da masu hali su kara aure don a taimaka wa zawarawan jihar kamar yadda suka fito suka roka a wata zanga-zanga da suka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata.
Gwamna Yari ya ce bai dace a bar zawarawan a cikin mawuyacin hali ba, domin barin su cikin wannan halin zai iya jefa su a cikin hadari, kuma zai taimaka wajen karuwar fasadi a jihar.
Wannan kira ya jefa jama’ar jihar cikin tunani musamman yadda Gwamnan ya yi kira ga ’yan majalisarsa su taimaka musu, inda ya kawo cece-ku-ce a jihar har wasu na cewa Gwamnan yana nufin kowane Kwamishina da masu ba da shawara su kara aure.
Sai dai kalamin na Gwamnan ya yi wa zawarawan dadi, kamar yadda wata daga cikinsu mai suna Malama Amina ta shaida wa wakilnmu: “Wallahi da za a aiwatar da abin da Gwamna ya ce da sun yi matukar taimaka mana, domin yadda muka matsu da son auren nan a yanzu ba sai mai hali ba. Kuma mun so ya zama duk wadda kake so ko take sonka idan an yi bincike kuma kun yi gwaji a asibiti a tallafa muku da abin auren da abinci daidai gwargwado, kuma a ja kunnen kowaccenmu ta yi hakuri idan an yi auren,” inji ta.
A ranar Alhamis da ta gabata ce zawarawa dubu takwas suka yi zanga-zanga don bayyana abin da ke damunsu na rashin maza, suna kiran gwamnatin Jihar Zamfara ta tallafa musu. Matan wadanda suka fito tun misalin karfe 8:00 na safe don yin zanga-zangar lumana sun bukaci gwamnatin jihar ta yi koyi da ta Jihar Kano wajen yi musu aure.
Zawarawan sun yi tattaki zuwa ofishin Hukumar Hizba ta Jihar don isar da sakonsu ga gwamnati inda suka ce sun kunshi wadanda mazansu suka sake su da wadanda aka kashe mazansu ko suka mutu, sai kuma ’yan matan da ba su samu mazan aure ba.
Shugaban kungiyar Zawarawan na Jihar Alhaji Sa’idu Gwashe ya shaida wa manema labarai cewa sun samu nasarar yi wa zawarawa 5,380 rajista, 2,200 wadanda mazansu suka rasu, 1,280 kuma ’yan matan da ba su samu mazan aure ba.
Shugaban ya ce babu abin da suke bukata sai a taimaka a sama musu mazan aure ko su su nemo gwamnati ta dauki nauyin auren kamar yadda ake yi a Jihar Kano, “Kuma in Allah Ya yarda zawarawan za su bi ka’idojin da gwamnati za ta sanya musu,” inji shi.
Sai dai wasu jama’a na ganin zanga-zangar abin bakin ciki ne domin a cewarsu ya kamata gwamnatin jihar ta rika gudanar da shi ne ba sai zawarawan sun fito sun koka ba.
Wata mai suna Malam Jamila ta ce shekaranta biyar babu miji, kuma babu mai zuwa wajenta da sunan aure, sai dai masu nemanta da lalata, kuma gata da ’ya’ya hudu. “Wani abin bakin ciki shi ne ga ni da budurwa a gabana, kuma samari ba su nufin komai sai karya, masu son auren kuma ba su da kudi” inji ta.
Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Malam Atiku Babalare Zawiyya ya ce a nasu bangaren za su gabatar wa gwamnatin jihar da koken zawarawan, “Wannan abu ne mai kyau matuka don zai rage aikata barna a cikin jihar, kuma suna fata gwamnati za ta dubi al’amarin don ta taimaka musu,” inji shi.
…Dagaci ya nemi gwamnatin Bauchi ta fara aurar da zaurawa
Daga Mu’azu Hardawa, Bauchi
Dagacin Tumu da Narabi da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Modibbo Usman Jumba ya nemi Hukumar Shari’a ta Jihar ta hanzarta aiwatar da shirinta na aurar da zawarawa don a tallafa wa iyaye da matan da ba su da hali saboda matsalar rashin kudi da ake fuskanta a yanzu.
Alhaji Modibbo Jumba ya bukaci haka ne a hirarsa da wakilinmu inda ya yaba wa shugaban hukumar Alhaji Mustapha Baba Ilela kan shirin hukumar na bin sahun wasu jihohin Arewa da suke aurar da zawarawa don tallafa wa ma’auratan da kayan bukata.
Ya ce shirin abin a yaba ne, kuma zai rage yawan matan da suke bukatar aure amma talauci ya hana iyayensu aurar da su da kuma mazan da ke bukatar aure amma rashi ya hana su yi.
Ya yaba wa hukumar shari’ar kan ayyukan sasanta jama’a da take yi, ya ce hakan ya taimaka wajen rage zuwa kotu da ofisoshin ’yan sanda. Ya ce hukumar ta kuma taimaka wajen hana rigingimu da ayyukan masha’a saboda samamen da ’yan Hizba ke kaiwa gidajen karuwai da na shaye-shaye.
Sai ya roki jama’a su bayar da goyon baya ga hukumar shari’ar don ta ji dadin gudanar da ayyukan da take yi na gyara tarbiyyar jama’a.