Zango bai boye wata ’yar fim ba – Arewa, MOPPAN

Kwana nan ne wata mata da ake kira Mama Uwani ta shiga wani gidan rediyo a Jihar Kano, ta ce fitaccen jarumi Adam A. Zango ya boye wata yarinya da take riko mai suna Rahama Nazeer, inda ya rika sanya ta a fina-finansa tsawon kwana arba’in, sai dai jarumin da kungiyoyin ‘yan fim da suka […]

Zango bai boye wata ’yar fim ba – Arewa, MOPPAN

Rahama Nazeer lokacin da ta daga kyautarta lokacin bikin Kwankwansiyya Award Kwana nan ne wata mata da ake kira Mama Uwani ta shiga wani gidan rediyo a Jihar Kano, ta ce fitaccen jarumi Adam A. Zango ya boye wata yarinya da take riko mai suna Rahama Nazeer, inda ya rika sanya ta a fina-finansa tsawon kwana arba’in, sai dai jarumin da kungiyoyin ‘yan fim da suka hada da Arewa Film Makers da MOPPAN sun karyata zargin, inda suka ce zance ne da ba shi da tushe ballantana makama.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an ji Mama Uwani tana cewa ba ta ga Rahama Nazeer ’yar shekara 11 tsawon kwana arba’in ba, inda hankalinta ya tashi, ta kuma rasa inda za ta dosa, daga baya ne ta ji labarin wai Adam A Zango ne ya boye ta a gidansa. Ta nemi ganinta amma hakarta ba ta cim ma ruwa ba, hakan ya sanya ta shiga gidan rediyo don ta sanar da halin da ake ciki, al’amarin da ya sanya zancen ya karade ciki da wajen industiri, inda kuma jama’a suka rika fadin albarkacin bakinsu.
Sai dai kuma masu ruwa da tsaki a masana’antar fim din Hausa (Kannywood) a karkashin kungiyar Arewa (AFMAN) da MOPPAN sun karyata zargin, inda suka ce Adam A Zango bai boye wata ‘yar fim a gidansa ba.
A yayin da yake zantawa da manema labarai Sakataren kungiyar MOPPAN Ahmad Salihu Alkanawy ya ce lokacin da suka samu labarin zargin da matar ta yi, sai suka binciki maganar inda suka gano cewa yarinyar ta dade a cikin masana’antar tun shekarar 2011, wanda kuma hakan yake nuna cewa ta fito a fina-finai da dama, wanda a cewarsa hakan ya karyta zargin matar na cewa yarinyar ta shiga fim ne ba tare da amincewarsu ba.
Alkanawiy ya ce bincike ya tabbatar ita matar da ke yin wannan zargi ita ce da kanta ta dauki Rahama Nazeer ta kuma kai ta gidan Ali Nuhu da nufin a sanya ta a fim, inda Ali Nuhun ya shaida musu cewa ba shi da wurin sanya ta a cikin fina-finansa, inda a cewar Alkanawiy matar ta kai yarinyar wurin Adam Zango ta hanyar wani mai suna Nazeer wanda shi ne kamar ubangidanta. “Abin takaici ne a ce saboda dan wani abu na bambanci ya sanya wadannan mutane su kirkiri karya tare da yada ta don bata sunan masana’antar fim. Mun gano cewa tsakanin ubangidan yarinyar wato Nazeer da kuma ’yar uwarta wato Mama Uwani sun samu rashin jituwa a kan wasu abubuwan yarinyar.”
Alkanawiy ya kara da cewa “Wannan yarinyar da ake magana akanta fa har lambar yabo ta karba a bikin fim na  Kwankwasiyya, inda aka ba ta talabijin din bango, duk da wannan suna nufin cewa ba su san cewa ’yarsu tana yin fim ba? Ko suna nufin cewa talabijin din da ta samu ta sayar da shi ne kafin a kai musu? Idan kun duba za ku ga cewar wannan zargi karya ne marar tushe wacce aka kulla don a bata sunan masana’natar fim din Hausa gaba daya, wanda mu kuma a matsayinmu na shugabanni ba za mu bar abin ya wuce haka nan ba tare da daukar matakin da ya kamata ba ta hanyar sanar da jama’a game da gaskiyar abin da ya faru, wannan shi ne abin da muke yi a yanzu.” Inji Alkanawi.
Shi ma a nasa bangaren Shugaban kungiyar AFMAN wadda aka fi sani da Arewa, Isma’ila Afakallah ya bayyana zargin wannan mata da cewa karya ce marar tushe don a bata sunan wannan masana’anta take da shi. A cewarsa “kungiyarmu ta Arewa ba ta ji dadin abin da wannan mata ta yi ba. Dukkaninmu mun san cewa wannan yarinyar ta dade tana fitowa a fina-finai tsawon shekaru biyu har ma ta samu kyautar lambar yabo ta bikin fim na Kwankwasiyya saboda wata fitowa da ta yi a fim din ‘Ummi’. Haka kuma duk fitowar da yarinyar take yi a fim mun tabbatar bai yi karo da ’yancinta a matsayinta na yarinya ba, sannan mun dauki alwashin kare mata mutunci. Wadanda suka kawo ta masana’natar fim sun nuna cewa ita marainiya ce wacce ke bukatar taimako, sai kuma ga shi sun zo da zargi.” Inji Afakallah.
Mai magana da yawun jarumin, Abu Sarki ya ce, daga taimako sai Zango yake neman shiga tsomomuwa.
Ya ce: “Tun da farko an kawo yarinyar hutu ne gidan Adamu. Yana son son yara kuma ba wannan ne lokaci na farko da yara ke zuwa hutu wurinsa ba, bayan yarinyar ta zo hutu sai furodusoshi suka nemi ta yi fim, amma Adamu ya ki har sai da ya samu izini daga ubangidanta Yaseer, bayan ta kammala fina-finan ne, ni da Adamu muka mayar da ita Kano, sannan muka danka ta a hannun Yaseer.”
Ya ce, abin mamaki bayan sun bar Kano sai suka samu labarin wata ta shiga gidan rediyo tana ta babatu a kan Zango.
Da wakilinmu ya tambaye shi ko akwai alaka tsakanin Adamu da yarinyar sai ya ce akwai amma yanzu ba zai komai a kai ba sai nan gaba.   
Wani na hannun damar jarumin mai suna Falalu dorayi wanda darakta ne ya ce  duk abin da jarumin ya yi wa wannan yarinya ya yi mata ne saboda Allah, sai dai kawai ’yan uwanta suna rigima ne kan dan abin da yarinyar ke samu a matsayinta na ‘yar fim. “tun farko shin Adam shawarar ya bayar cewa yarinyar ta koma makaranta, inda har ya yi alkawarin daukar nauyin karatunta; sai ga shi sun saka masa ta wannan hanya, sai dai kuma Allah Zai yi hukunci a tsakaninmu” Inji shi.
Aminiya ta nemi sanin ko kungiyoyin za su dauki wani mataki na shari’a a kan lamarin sai suka bayyana cewa, tun da maganar na gaban Hukumar da ke kula da fataucin mutane ta NAPTIP, za su jira su ji abin da hukunci zai yi.
Aminiya za ta ci gaba da bin labarin don kawo muku yadda al’amarin zai kasance.