Zango ga furodusoshi: Na daina fitowa a fim din da bai fi Naira miliyan biyu ba
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya ce ya daina fitowa a cikin duk wani fim mai kasafin Naira miliyan biyu a matsayin akita a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.Jarumin wanda Jakadan Kamfanin MTN ne ya bayyana haka ne wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi da karfe 11:00 […]
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya ce ya daina fitowa a cikin duk wani fim mai kasafin Naira miliyan biyu a matsayin akita a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.
Jarumin wanda Jakadan Kamfanin MTN ne ya bayyana haka ne wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi da karfe 11:00 na safe.
Sanarwar wadda ya yi ta cikin Ingilishi, ya hada ta da wani hoto da ya rataya kyamara a wuyansa, ya yi mata take da budaddiyar wasika ga furodusoshi, ya ce, ya yanke wannan hukunci ne don ba jarumai masu tasowa dama, inda hakan zai sa masana’antar Kannywood ta habaka kamar yadda takwarorinta a duniya irin su Hollywood da Bollywood suka bunkasa.
Jarumin ya ba dukkan wadanda wannan sanarwa ta bakanta wa rai hakuri, inda ya nanata cewa bai yanke hukuncin don cin zarafin wadansu ba, sai don hakan ne zai haifar wa Kannywood da mai ido.
Ga abin da sanarwar ta kunsa: “Budaddiyar wasika, furodososhin Kannywood, na daina fitowa a fim mai kasafin Naira miliyan biyu a matsayin akta. Ya kamata mu ba jarumai masu tasowa dama, inda hakan zai sa mu kasance kamar sauran masana’antun fina-finai irin su Bollywood da Hollywood. Ina ba da hakuri idan wannan bayani ya bakanta wa wani rai a cikin abokan sana’ata.”