Zango ya zama jakadan kamfanin MTN

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya yi wa Kamfanin sadarwa na MTN talla bayan ya zama jakadansa.Jarumin ya je Legas a makon jiya don daukar tallar farko a karkashin kamfanin tun bayan da ya sa hannu a kwangilar jakadancin kamfanin watanni uku da suka gabata.Mai magana da yawun jarumin, Abu Sarki ya ce,  […]

Zango ya zama jakadan kamfanin MTN
Zango ya zama jakadan kamfanin MTN

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya yi wa Kamfanin sadarwa na MTN talla bayan ya zama jakadansa.
Jarumin ya je Legas a makon jiya don daukar tallar farko a karkashin kamfanin tun bayan da ya sa hannu a kwangilar jakadancin kamfanin watanni uku da suka gabata.
Mai magana da yawun jarumin, Abu Sarki ya ce,  jarumin ya je Legas don yi wa kamfanin talla ne ba wai don sa hannu a kwangilar jakadanci tsakaninsa da kamfanin ba.
Ya ce “Ba wai don sa hannu muka je Legas ba, a’a, mun je ne don daukar tallar kamfanin na bidiyo mai suna ‘100% MTN Bonus’. Watanni uku da suka wuce ne jarumin ya sanya hannu amma daga baya aka samu matsala.
“Mun riga mun gama sa hannu a kwangilar zama jakadan kamfanin sadarwa na MTN tun ba yanzu ba, daga baya sai wadansu abubuwa suka biyo baya, kasancewar mun yi mantuwa yayin cike fom din kwangilar, hakan ya haifar da matsala. Daga baya aka fasa yarjejeniya ta farko, sannan aka yi sabuwa ta shekara daya. Hakan ya zama mana alheri.” Inji shi.
Ya ce kamfanin ya fada wa jarumin ayyukan da zai yi wadanda suka hada da: halartar galar kamfanin (show), wanda za a yi sau 10 a shekara; zai rika yi masa tallace-tallace, sannan idan ana gudanar da wata gasa kamar kwallon kafa ko Polo za a gayyaci jakadun MTN su rika tallata masa hajarsa.
Ya ce bayan shekara za a ga yiwuwar sabunta ta ko akasin haka.
Ya ce “Ba a sanya wa jarumin wani buri da ake so ya cimma bayan wadanda suka zayyano a cikin fom din da ke dauke da yarjejeniyar ba, don haka bayan shekara daya za mu ga yiwuwar sabunta ta ko akasin hakan.”
Ya ce wannan babbar nasara ga masana’antar fina-finan Hausa idan aka kalli yadda duniyar nishadantarwa ta ci gaba, “MTN ba babban kamfanin sadarwa ne a duniya, amma ya nemi Adamu ya zama jakadansa, wannan babbar nasara ce ga jarumin da MTN da kuma Kannywood.”
Ya ce: “A da za a ga masu tallar kamfanoni ba Hausawa ba ne, idan wani yana jin Hausa kawai sai ya rika yi musu talla, inda za ka ga tallace-tallacen cike da kura-kurai barkatai. Amma yanzu sakamakon Kannywood komai ya fara canjawa.”
A karshe jarumin ya bukaci masoyansa su ci gaba da ba shi goyon baya don ya kara jajircewa wajen shirya fina-finai masu fadakarwa da kuma nishadantarwa.