Zantukan zarar Zaira
A majigin kyautata rayuwa ’Yan lalle na karuwa Adon gari na moruwa Amarsu na dada soyuwa Agogon ango na juyuwa A a Akwakun Arewatawa Ana ganin tariyar Turkawa Gadar adon-gari mai kayatarwa Kai-kawon ’yan lalle ba kakkautawa Tamfar damar karamin laujen Mekzikawa Zakuwar zakakura Zakalkalewar zankakurin zakara Zumun zaman Zaira Zilliyar zarra Zumudin […]
A majigin kyautata rayuwa
’Yan lalle na karuwa
Adon gari na moruwa
Amarsu na dada soyuwa
Agogon ango na juyuwa
A a Akwakun Arewatawa
Ana ganin tariyar Turkawa
Gadar adon-gari mai kayatarwa
Kai-kawon ’yan lalle ba kakkautawa
Tamfar damar karamin laujen Mekzikawa
Zakuwar zakakura
Zakalkalewar zankakurin zakara
Zumun zaman Zaira
Zilliyar zarra
Zumudin Zahara
Zancen zumuncin ziyara
Zirin azara
Zogin zungura
Zazzagar zabura
Ziryar zungureriyar zabira
Majigi
Mata da miji
Suna ta cin naman kaji
’Ya’ya na sa su bugun kirji
Mirgina-mirginar magagi
Akwakun Arewatawa
Karamin laujen tsayuwar kafa guda
Soyuwar zukata tai gargada
Magabta na gada-gada
Sun ga walkiya da tsawa
Turka-turkar Turkawa
Tarairayar ’ya’ya da uwa
Turancin Turawa
Turereniyar tunkudewa
Tarnakin takurawa
Kurtun halo alalo
Ya zam akwakun kallo
Fina-finan soyayya salo-salo
Kulelen Kululu kilo-kilo
Zinariyar Zaira ta azazzalo
Facakar facala
Fal-fal din fitila
Falo-falo falla-falla
Falle fululun shafuka falala
Kisisina
Kishiya ce karshen magana
Kashe wutar wauta a dangana
Karsashin nuna tsana
Karambanin karon bauna
Kutungwila
Sai masu hila
Zancen kila-wa-kala
Rashin tabbacin lalala
Sai masoya su hassala
Wasan kwaikwayo
Aikin dan koyo
Yai wa Bab oyoyo
Balaguro aka bibiyo
Batutuwa aka liliyo
Al’adun mutan Gabashi
Mun dubi Turai a Yammaci
Rashin daukar komai da muhimmanci
Bahaushe mai ban haushi
An biyoka bashi
A yunkura tashi
Innuwar hutu kar ai kashi
Kyawawan ta’adu ai tushi
Kowa ya inganta nashi
Ban da kai wa juna naushi
A tada kai da matashi
Jariri sai lallashi
Amarya sai da kunshi
Ango yai ta murmushi
Aure sai da toshi
A kasafta albashi
Ciyar da iyali ba fashi
Uwargida ban da fushi
Ai annashuwa da karsashi
Farka ki ce wa miji tashi-tashi
In kai zubin adashi
Kwaso mu ci dashishi
A zuba mai da tasshi
Duk mai so a sammashi
Almajiri ya miko kokonshi
Wa-ka-ci-ka tashi
Ko mai neman bashi
An ci masa albasa mai lawashi
An tuka tuwon laushi
Gutsuro lomar geffan sashi
Takun saka ya kare
Nuku-nuku an karkare
Magabta sun dare
Masalaha ta sa kowa ya dire
Hirar rana zuwa dare
Farfar da fure
Furanni farare
Fikar fere-fere
Fankata-fankantan faya-fayan furfure
Fur tashin tsuntsun tsirin tsere
Dimbin masu baje na-mujiyarsu a AKWAKUN AREWATAWA NA KARAMIN LAUJE DA TSAYUWA BISA KAFA GUDA, sun saba kallon majigin mirgina-mirginar zamantakewar rayuwar Turkawa, musamman na MALAMA NISA DA KYAUTATA RAYUWA inda aka yi ZANTUTTUKAN ZARRAR ZAIRA, wata jaruma ’yar talakawa da ta samu soyyyar ATTAJIRI DAN ATTAJIRI,wanda ya yi mata toshi, har ya turke ta a matsayin AMARSU TA ANGO.
Wannan majigi na wasan koyi ka koyar ya nusar da Haurobiyawa tsarin zamantakewa da turka-turkar takun sakar Turkawa kafin su zamo ma’aurata. Domin su ma al’ummar Gabashi da na Yammacin duniya sukan yi fama da KISISINAR KISHIYA, kodayake dai sun fi yin karon-batta da FACAKAR FANCAL-FANCAL DIN FACALA.
Hakika shirye-shiryen AKWAKUN AREWATAWA mai wutsil-wutsil din hotuna yana matukar kayatar da Haurobiyawa, musamman masu yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare da sai-in-sa ba, don haka ma tashar akwatin magana mai wulkita hotunan ke yin faskaren ma’anonin kalallame kalaman Indiyawa da Larabawa da na Turkawa, har ma da na masu murguda baki kamar suna cin kilishi, su kanga gilashi su yi ta yaren Ingilishi, don samar da kiraren nunin fahimtar da Haurobiyawa kan al’amuran rayuwa.
Batu na ingarman karfen karafan kwangirin tarago, ba tare da bata lokaci ko jan kafar wulwulawar agogo ba, ina fatan ’yan wasan majigin KANNEN-AUDU da ke shirya fina-finai a Arewacin Haurobiya sun dauki darasi, musamman ma jin cewa sun kai wa Baban-burin-huriyya ziyarar ban girma.
Lallai akwai bukatar ’yan wasa da jaruman fina-finan KANNEN-AUDU su rika shirya majigin nusar da al’umma yadda za a warware tsilli-tsilli matsalolin da ke ci wa Haurobiyawa tuwo a kwarya, musamman al’amuran da suka shafi ZAMAN-TAKEWA DA SIYASAR YASAR HAURO DA TATTALIN TUTTULE TULUN TARIN DUKIYA.
Ina ganin aiwatar da managartan tsare-tsare a shirye-shiryen wasan majigin KANNEN-AUDU za su inganta harkokin koyon watsattsake da buga wagagen littattafai, tare da nishadantar da al’umma, ta yadda kowa zai samu annashuwa da karsashin baje na-mujiya da zarar batutuwan jarumanmu sun zarta ZANTUKAN ZARRAR ZAIRA, wadda ake ta nuna mana a AKWAKUN AREWATAWA na karamin lauje da tsayuwa bisa kafa guda.