Zantuttukan hikima domin kyautata rayuwa (1)
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku sallama, Assalamu alaikum warahmatullah! Ina ba ku hakuri, kasancewar na tafi hutun wata daya cur, alhali ban sanar da ku ba. A halin yanzu na dawo, don haka za mu ci gaba da musharaka da juna, musamman ta hanyar zizara wa juna sinadaran […]
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku sallama, Assalamu alaikum warahmatullah! Ina ba ku hakuri, kasancewar na tafi hutun wata daya cur, alhali ban sanar da ku ba. A halin yanzu na dawo, don haka za mu ci gaba da musharaka da juna, musamman ta hanyar zizara wa juna sinadaran rayuwa, domin kyautata rayuwarmu ta yau da kullum, tare da neman dace a yau da kuma gobe, idan lokacinmu ya zo. Allah Ya ba mu ikon cin gajiyar rayuwarmu kuma mu dace da kyakkyawan karshe, amin.
A yau kuma za mu bude shafin ne da sabon maudu’i, inda za mu zakulo wasu zantuttuka na azanci da hikima, domin mu yi amfani da su wajen inganta al’amuranmu na rayuwar yau da kullum. Da fatan Allah Ya yi mana gamo da katar, amin.
Aiki da hankali, ya fi aiki da agogo: Wannan dadadden zancen hikima ne kuma abin lura ne a rayuwarmu. Har kullum mutum ya sanya a ransa cewa, duk abin da zai aiwatar, to ya yi tunani sau biyu ko sau uku, kafin ya aiwatar da shi. A nan, ba batun aiki kadai ba, hatta kalaman da za su fito daga bakinka, su kasance ka jinjina su, ka tauna su, sun kai sun kawo a tunaninka, kafin ka furta su. Idan ka yi haka, to ka yi aiki da hankali, domin kuwa duk aikin da ka yi bisa tunanin abin da zai je ya zo, to zai kasance ingantacce kuma zai kasance amsasshe ga al’umma. Sanin cewa babu wani aiki da za a gudanar tare da sanya kyakkyawan nazari da tunani da zai zama na assha.
Haka batun yake idan an zo wajen kalami ko furuci, nan ma, ya zama dole mutum ya yi aiki da hankali. Abin sani shi ne, harshenka shi ne linzaminka, kuma ana gane kamalar mutum da muhibbarsa ta hanyar furucinsa. Babu mai furta kalmomin kirki sai mutumin kirki. Idan ka ji maganar banza ko ta ashararanci ta fito daga bakin mutum, to ka tabbata, kada ka raba daya biyu, shi asharari ne, mutumin banza ne. Ba wani abu ya ba shi wannan shaida ba sai wannan furuci nasa na banza, na ashararanci. Don haka, a kodayaushe, mu sanya hankali da tunani kafin aiwatar da duk wani lamari, kafin furta kowace irin kalma daga bakunanmu.
Kada ka tambayi maraya “ina mahaifinka?” Kai daga jin an ce wane maraya ne, ai ya kamata a ce ka san makomar mahaifinsa, domin dai ba a kiran mutum maraya sai mahaifinsa ya mutu. Idan ka tsaya bata lokacin neman inda mahaifin maraya yake, ka dauki hanyar da ba ta dace ba kuma ka dauki hanyar bata wa kanka lokaci, wanda hakan zai hana ka aikata abin da ya dace a daidai wannan lokaci. Me ya dace da maraya? Taimako, tallafi, rarrashi da sauran ayyukan alheri makamantansu.
Wannan zancen hikima yana nuna mana wani darasi a rayuwa, watau kada mutum ya aikata abin da bai dace ba a kowane lokaci. Idan misali kana hanya kan tafiya, sai ka ga wani mai abin hawa ya yi hadari, ga shi kwance cikin jini yana neman agajin farko, shin me ya kamata ka yi? Za ka tsaya tambayon yadda aka yi ya yi hadarin ne? Za ka fara binciken shi wane ne ko kuma daga inda ya fito? Idan ka yi haka, kamar ka tsaya tambayon maraya inda mahaifinsa yake ne. Ma’ana, ka tsaya yin abin da bai dace ba, ka tsaya bata lokaci, ka tsaya yin sakacin da zai haifar da barna. Ka ga ke nan, kamata ya yi ka yi gaggawar ba mutumin nan taimakon farko, yadda zai samu sa’ida.
A rayuwa, kada ka ce wa bazawara “me ya kashe aurenki?” Kai dai nemi hanyoyin da suka kamata ka taimaka mata. Idan kuwa ka tsaya neman bahasi, to kamar ka tsaya tambayar maraya inda mahaifinsa yake ne. Idan za ka taimaki fakiri ko mabukaci, kada ka ce masa, “ko kana da bukata?” Wannan bata lokaci ne, kuma ba ta’ada ce ta kirki ba. Kamar ka ce wa bakonka ne, “za ka ci abinci?’ Ka ga kuwa wannan tambayar ba ta dace ba, kamata ya yi kawai ka kawo masa abinci, shi ne karimci kuma abin da ya fi dacewa. Ya rage ruwansa ko ya ci abincin ko kuma idan ba ya bukata, zai ayyana da kansa. A kullum dai mutum ya tunkari yin abin da ya dace da kamala, kada ya rika yin abu ba tare da lissafi da nazari ba. Ita rayuwa ’yar natsuwa ce da hankali, akasin haka kuwa na haifar da halayya marasa kyau.
Za mu ci gaba