Zantuttukan hikima domin kyautata rayuwa (2)

Ya ma’abuta bibiyar Sanadarin Rayuwa, assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Ina yi muku fatan alheri a wadannan kwanaki masu albarka, a wannan muhimmin wata na Zul-Hajji. Kamar yadda muka faro sabon maudu’i a makon jiya, yau za mu ci gaba da zakulo wasu zantuttuka na azanci da hikima, domin mu yi amfani da su wajen inganta […]

Zantuttukan hikima domin kyautata rayuwa (2)
Zantuttukan hikima domin kyautata rayuwa (2)

Ya ma’abuta bibiyar Sanadarin Rayuwa, assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Ina yi muku fatan alheri a wadannan kwanaki masu albarka, a wannan muhimmin wata na Zul-Hajji. Kamar yadda muka faro sabon maudu’i a makon jiya, yau za mu ci gaba da zakulo wasu zantuttuka na azanci da hikima, domin mu yi amfani da su wajen inganta al’amuranmu na rayuwar. Da fatan Allah Ya yi mana gamo da katar, amin.
Masu hikimar zance sun ce, duniya makaranta ce, mutane ne dalibanta. Tsantsar gaskiyar wannan zance ba ya misaltuwa, domin kuwa ga darasin nan karara kowa yana gani. Kullum rayuwar mutum cikin koyon al’amura take. Idan ka sanya lura, duk wata mu’amala da ta gudana tsakaninka da wani ko wata, za ka ga cewa dauke take da darasi.
Abin da ka aikata ko ka ambata yanzu, babban darasi ne ga abin da zai faru an jima ko  gobe, ko shekara ko shekaru masu zuwa. Haka kuma abin yake ga mutanen da suka rayu a can baya. Duk abin da suka aikata a jiya, ko shekarun da suka rayu komai yawansu, darasi ne ga al’ummar yau.
Tarihi cike yake da sakamakon abubuwan da suka faru a jiya. A duk lokacin da ka ji labarin wani mutumin kirki, za ka iske cewa ya samu sakamako mai kyau tun a nan duniya, ko ba komai za ka ji al’ummar yau tana yabonsa da yi masa addu’ar kirki. Idan ma ya bar magada, za ka ga ana son su, ana nuna musu kara da taimako a duk lokacin da suka bukaci haka.
Haka shi ma wanda ya kafa tarihin aikin banza ko shashanci a baya, za ka samu tarihinsa a gurbace. Za ka ji yadda ya yi karkon kifi, rayuwarsa ta kare cikin hallaka. Tun daga tarihinsa za ka ji mutane suna yi masa mummunan hisabi a nan duniya. Idan ya bar magada kuwa, za ka samu suna girbar abin tsiyar da ya aikata. A yau din nan, da an ambaci sunan Fir’auna, mutanen kirki za ka ji suna la’antarsa. Ko a nan kusa, da zarar an ambaci sunan Maitatsine, wadanda suka san tarihinsa za ka ji sun biyo da la’ana.
Babban abin da wannan ke nuna mana shi ne, mu rika daukar darasi daga al’amuran da suke faruwa yau da kullum. A duk lokacin da za mu aikata wani abu, to mu rika yin koyi da magabata na kirki, mu guji aikata miyagun ayyuka, irin wadanda mugaye suka aikata a baya. Idan mun yi kuskure jiya, to ya zame mana darasi, kada mu sake aikata shi a yau. Duniya dai makaranta ce, mutane ne dalibanta. Haka kuma a wannan babbar makaranta ta duniya, mu fahimci cewa rayuwar da ke gudana cikinta, ita ce dakin karatu, alhali kuma babban malami, shi ne lokaci.
Kullum lokaci shi ne jigon da ke tafiyar da kowace irin rayuwa, domin kuwa duk abin da ke wakana, a cikin lokaci yake wakana. Da zarar ka aikata wani abu mai muhimmanci, wanda ka ci ribarsa, a daidai wannan lokaci za ka shaida haka, kuma ka rike shi ke nan. Idan al’amarin babba ne, wanda ya shafi al’umma, su ma za su shaida wannan lokaci, ya zama abin koyi da ishara a kowane zamani.
Wani zancen kuma abin dubawa shi ne, mu lura da rayuwar duniya, mukan hadu ne a matsayin baki, sannan mu rabu da daidaya. Ba sai mun yi nisa ba za mu fahimci darasin wannan zance. Tun a zuwanmu duniya za mu ga cewa jariri daya ake haihuwa, da sannu ya girma har ya zama cikakken mutum. Shi daya ya zo duniya, amma da sannu zai zama iyali, shi ma wadansu yaran su fito daga gare shi. Sannu a hankali sai ka ga gida ya kunshi kakanni, iyaye, yayye, kanne, ’ya’ya da kuma jikoki.
Haka kuma, idan an zo rabuwa, da daidai ake rabuwa. Ko babu mutuwa akwai hijira kuma akwai samun madogara. Haka saurayi zai fita daga gidansu ko daga garinsu zuwa wani da nufin aiki ko karatu ko sana’a. Ko ba wannan akwai mutuwa, wacce yadda muka zo daya-bayan-daya, haka za mu koma.
Darasin rayuwa da ya kamata mu fahimta daga wannan batu na azanci da ya gabata shi ne, a duk lokacin da muka samu kanmu a tare da wadansu, mu tuna da cewa ba dauwama za mu yi ba. Don haka, ka yi kokarin zama lafiya da fahimta da duk wanda Allah Ya hada ka da shi. Idan kuma kaddara ta sanya za a rabu, to a yi kokarin rabuwa lafiya da juna, cikin fahimta da maslaha. Tasirin haka shi ne, ba mu san lokacin da za mu sake haduwa da juna ba. Idan an yi rabuwar kirki, da zarar an hadu, abin kirki zai biyo baya. Idan kuwa rabuwar tsiya-tsiya kuka yi da mutum, to duk ranar sake haduwa, shaidar ba za ta yi alfanu ba. Babu mamaki ku bukaci taimakon juna.
A koyaushe dai mu kasance cikin sara tare da duban bakin gatari. Mu aikata alheri, mu tafiyar da rayuwarmu cikin fa’ida da fahimta.
Sai kuma makon gobe, in Allah Ya kai mu.