Zara ba ta barin dami

Najeriya dai ta zama babban kwabo a cikin kasashen Afrikan da ke yi mata kallon babbar yaya. Ta shahara game da ayyukan alheri da yawa, ta kuma yi kaurin suna  wajen tafka abubuwan tsiya. A takaice dai ana iya cewa Najeriya tamkar birgimar hankaka ce, kowa ya ga farinta sai kuma ya ga bakinta. A […]

Zara ba ta barin dami
Zara ba ta barin dami

Najeriya dai ta zama babban kwabo a cikin kasashen Afrikan da ke yi mata kallon babbar yaya. Ta shahara game da ayyukan alheri da yawa, ta kuma yi kaurin suna  wajen tafka abubuwan tsiya. A takaice dai ana iya cewa Najeriya tamkar birgimar hankaka ce, kowa ya ga farinta sai kuma ya ga bakinta. A ‘yan shekarunnan ba a jin komai game da Najeriya sai miyagun ayyukan da ‘ya’yanta ke tafkawa da kuma yadda manyansu ke daure masu gindi don ci gaba da aikatawa, ko yadda suke kawar da kai, ba su son tsawatawa.
Duk da cewa rashin tsaro ya zame babbar matsalar da aka kasa magancewa, hakan kuma ya hana jama’a walwala da walawa, kuma birane da kauyuka ba wani mai sauran sakewa, sai ga wata sabuwar matsala ta kunno kai, sa’annan aka bari ta yi kamari, ta zame tamkar wutar dajin da aka kasa kashewa. Ai da ma haka nan miyagun al’amura ke faruwa a Najeriya, kaman kurjin da kan zame wagegen gyambo ne a kafar kazamin da ba ruwanshi da neman magani cikin dan  kankanin lokaci sai ya yi ta kwakkwabewa. Tun ana cewa ‘yan  ku-ci-ku-ba-nin ta’addanci na hana kamfanonin Turawa hakan danyen mai a yankin Neja Delta ba wani damuwa, sai ga shi nan sun rika, sun zama kasaitattun ‘yan fashin da ba mai iya tunkara, sun kuma mayar da dukiyar kasar tamkar ta gadon kakanninsu su kadai.
To idan har wasu ‘yan ta’adda, tagajan-tagajan, za su iya wa-ka-ci-ka-tashi da dukiyar kasa, me zai hana wadanda suka fi su kwarewa da gwanancewa a wannan sabgar taka rawar da za ta fi tasu armashi?  Tun da farko dai babu yadda za a ce ba tare da sanin manyan yankin Neja ne ba ake farfasa bututun  mai na kamfanonin kasashen ketare don zuko mai don tacewa a haramtattun matatun cikin gida, a kuma fitar da shi kasashen ketare don sayarwa; ana kuma bayar da kariya ga jiragen ruwan da ake loda danyen man da aka jida daga haramtattun rijiyoyin mai zuwa kasashen waje. To idan kuwa har wasu karabiti na iya yin haka, me zai hana jiga-jigan shugabannin yankin da kuma dakarun hafsoshin tsaro ba za su yi uwa, su yi makarbiya ba cikin wannan al’amari, domin kuwa idan har su ne za su yi ruwa-da tsaki wajen satar dukiyar kasar haihuwarsu akwai wani dan da ‘ya mace ta tsuguna, ta haifa, da zai samu damar muzguna masu, balle har ya yi galba a kansu?
Ba shi ke nan ba! Sai kawai wadannan shugabanni da jami’an tsaro, suka ara, suka yafa, har daga bisani suka hana mai kora shafawa, domin kuwa sun dukufa gadan-gadan wajen satar danyen man ba kakkautawa. Wannan al’amari ya yi kamari ne tun a shekarar 2011, sa’ilin da Shugaba Goodluck da jama’arsa suka danki ragamar mulki. A sakamakon haka ne kasar ta shiga asarar zunzurutun kudi har dalar Amerika miliyan dubu shida (kwatankwacin Naira miliyan dubu 990 a kowace shekara.) A wannan lokaci ne kuma zirga-zirgar jiragen ruwan ‘yan ta’adda ya yawaita a yankin Gulf of Guniea (yankin da ya yi iyaka da kasashen Najeriya, Bakassi, Ekuitorial Guinea da kuma Angola, wadanda ke da dimbin arzikin man fetur), inda ake sace danyen mai zuwa haramtatun matatun mai a kasashen Ghana da  Kwatdibowa da kuma Rasha. Rahotanni sun ce tabargazar da ke wanzuwa a wannan yankin dangane da fashin jiragen ruwan mai na halatattun gwamnatoci ya dara badakalar da ake yi irin haka a gabar tekun kasar Somalia, inda ‘yan gwagwarmaya ke tare jiragen ruwan Turawa, suna addabar su da sace-sace.
Wannan al’amari ya buwayi gwamnatin Najeriya, wacce ta gamu da batar basira wajen shawo kan matsalar da ta bari ta gagare ta tun tana ‘yar karama. A yanzu ma abin kara tabarbarewa ya yi, domin kuwa har rundunan jiragen ruwa ta Najeriya ta ce ita dai ba za ta iya hana wannan mummunar sana’ar satar danyen man kasar ba, ba kuma za ta iya hana ficewa da shi kasashen ketare ba. A cewar rundunar askarawar jiragen ruwa tilas ne a hada da sojojin kasa da kuma na sama muddin ana son samun nasara.  Tikisa!! Wai dan-agaji ya ga gawar soja. Ashe ke nan ba rana balle watan maganin barayin danyen man Najeriya.  To amma tun kafin a kai ga haka Shugaba Jonathan ya taba tuntubar kasashen da ake kai man da ake sacewa daga kasar nan da su taimaka don dakile wannan dabi’ar. Sun kuma ce masa su ma ba za su iya ba, sai dai idan zai  zakulo manyan jami’an gwamnatinsa da kuma hafsoshin tsaro masu daure wa barayin man gindi, ya hukunta su, idan kuma ba haka ba, to sai ya kuka da kansa.
Dangane da haka ne gwamnatin tarayya ta tsara shirin ahuwa ga  ‘yan tsageran yankin don a tsira daga wadannan matsalolin da satar danyen mai, ta kuma tuttura shugabannin ‘yan ta’addan  wasu kasashen ketare don koyo dabarun kakkare bututun man daga harin ta’addanci, sa’annan kuma ta bayar da aikin kwangilar kula da  bututun mai akan Naira miliyan dubu goma sha biyar a kowace shekara ga wasu fitattun ‘yan ta’addan yankin guda biyu: Tom Polo da Ateke Tom, amma duk a banza.  Dukiyar mai da ke bizne a karkashin kasa na dukkan ‘yan kasar ne, bai kamata ba a kyale wasu ‘yan kalilan su dinga sacewa ba. Al’amarin  kamar damin hatsi ne rufe a cikin rumbu, wanda maigida ko waninsa ke yawan zara, to cikin dan kankanen lokaci zai neme damin, ya rasa. Tilas ne Gwamnatin Jonathan ta yi hattara don kada ‘yan lelenta su jawo wa kasar abin duniya da rana tsaka gagal.