Zargi: ’Yan sanda sun musanta sace tsohon Kwamishinan El-Rufai
El-Rufai ya zargi jami’an tsaro da ɗauke tsohon Kwamishinan ba bisa ƙa’ida ba.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta ƙaryata zargin da Tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya yi cewa jami’an tsaro sun sace tsohon Kwamishinansa, Jafaru Sani.
El-Rufai ya yi wannan iƙirari ne a shafinsa na sada zumunta cewa an ɗauke tsohon Kwamishinan kamar fursuna ba tare da bin ƙa’idojin doka ba.
- Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo
- Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi
Ya yi zargin cewa wata “ƙungiyar masu garkuwa da mutane” da ke da alaƙa da Gwamna Uba Sani ce ke da alhakin ɗauke tsohon Kwamishinan.
Da yake mayar da martani, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana zargin a matsayin ƙarya.
“Babu wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane a cikin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.
“Mu hukuma ce da ke aiki bisa kundin tsarin mulki don tabbatar da doka da oda,” in ji shi.
Ya buƙaci ’yan siyasa su guji yaɗa labaran da ba su da tushe.
“Yi wa jami’an tsaro ƙarya na iya haifar da ruɗani da kuma rage martabarsu. Idan mutum yana da ƙorafi, ya bi hanyar shari’a maimakon yaɗa kalaman da za su tayar da fitina,” a cewarsa.