Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman

Hukumar EFCC ce, ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda biyar.

Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman

Wata Babbar Kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ake tuhuma da almundahana.

A ranar Alhamis, Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin sakin Farfesa Usman daga gidan gyaran hali na Kuje bayan an cika sharuɗan belinsa.

Hukumar EFCC ce, ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗaɗe.

Ana zargin ya amince wajen sayen motoci a kan Naira miliyan 49.2 maimakon Naira miliyan 30 da aka ware a matsayinsa na shugaban NHIS a 2016.

EFCC, ta kuma ce Farfesa Usman ya bai wa wani kamfani mai suna Lubekh Nigeria Limited kwangilar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta Naira miliyan 17.5 ta hannun ɗan uwansa, Khalifa Hassan Yusuf.

Duk da haka, Farfesa Yusuf ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa.

Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura

Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero daga fadar Nassarawa

Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman

Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa