Zargin almundahana: Maina ya zo kotu a kujerar guragu

A jiya Alhamis ce tsohon Shugaban Hukumar Sake Fasalin Fansho, Abdulrasheed Maina ya je kotu a kujerar guragu bisa zarginsa da ake yi da almundahana. Hukumar EFCC ce take  tuhumar Maina da cin amana da almundahana da bude asusun banki da yawa da sunan wasu da sauransu. An sha daga karar bisa cewa Maina ba ya […]

Zargin almundahana: Maina ya zo kotu a kujerar guragu

Tsohon Shugaban Hukumar Fansho Abdulrasheed Maina zaune a kujerar guragu Hoto: Channels TV

A jiya Alhamis ce tsohon Shugaban Hukumar Sake Fasalin Fansho, Abdulrasheed Maina ya je kotu a kujerar guragu bisa zarginsa da ake yi da almundahana.

Hukumar EFCC ce take  tuhumar Maina da cin amana da almundahana da bude asusun banki da yawa da sunan wasu da sauransu.

An sha daga karar bisa cewa Maina ba ya da lafiya, sai jiya ya zo kotun a kujerar guragu.

Kotu kuma ta tura shi gidan kaso kafin a ci gaba da bincike.