Zargin batanci: Kotu ta ba da belin Dokta Idris Abdulaziz

Kungiyar Fityanul Islam ta maka shi a kotu bisa zargin batannci ga Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya karyata.

Zargin batanci: Kotu ta ba da belin Dokta Idris Abdulaziz

Dokta Idris Dutsen Tanshi

Kotu ta bayar da belin malamin Musuluncin nan, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ake zargi da furta miyagun kalamai ga Manzon Allah (SAW).

Kungiyar Fityanul Islam ce dai ta maka malamin a Kotun Majistare da Jihar Bauchi, bisa zargin sa da kalaman batannci ga  Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya musanta.

Kotun ta bayar da belin fitaccen malamin ne a ranar Talata bayan bukatar hakan da lauyoyin malamin suka nema.

A ranar Litinin ne, ’yan sanda suka gurfanar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi bisa zargin tayar da hankulan jama’a.

Lauyoyinsa sun shaida wa kotu cewa zargin da ake masa da aikatawa ba zai hana a bayar da shi beli ba, inda a ranar kotun kotu ta sanya Talata domin yanke a kan bukatar lauyoyin.

Sai dai a ranar alkalin kotun ya ba da umarnin a ci gaba da tsare malamin a gidan yari kafin zaman na ranar Talata.

Kotun ta bayar da belin malamin ne bisa sharuddain gabatar da wani babban ma’aikacin gwamnati da ya kai matakin babban sakatare da kuma mai unguwa ko hakimi su tsaya masa.

Za kuma su gabatar da takardar mallakar wata kadara da kimarta ta kai Naira miliyan biyar sannan dole ne masu tsaya masa su gabatar da hotunansu ga rijistaran kotu.

Allain kotun, Mai Shari’a Abdulfatah Shekoni ya daga sauraron shari’ar zuwa ranar Laraba 24 ga watan Mayu da muke ciki.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba