Zargin cin hanci da rashawa: Shugaban Hukumar FIFA ya sauka daga mukaminsa

A ranar Talata da ta gabata ne Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) Mista Sepp Blatter ya sauka daga mukaminsa bayan ya shafe kimanin shekara kimanin 17 yana shugabancin hukumar. Sannan ya sauka ne a kasa da mako daya bayan an sake zabarsa a matsayin Shugaban Hukumar a makon jiya. Shugaban ya sauka ne […]

Zargin cin hanci da rashawa: Shugaban Hukumar FIFA ya sauka daga mukaminsa
Zargin cin hanci da rashawa: Shugaban Hukumar FIFA ya sauka daga mukaminsa

A ranar Talata da ta gabata ne Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) Mista Sepp Blatter ya sauka daga mukaminsa bayan ya shafe kimanin shekara kimanin 17 yana shugabancin hukumar. Sannan ya sauka ne a kasa da mako daya bayan an sake zabarsa a matsayin Shugaban Hukumar a makon jiya.

Shugaban ya sauka ne bayan dambarwar cin hanci da rashawa da ta sarke hukumar bayan hukumomin tsaron Amurka suka kama jiga-jigan hukumar su kimanin 14 da laifin cin hanci da rashawa da aka kiyasta sun kai Dala miliyan 150 kwatankwacin Naira biliyan 33.
Mista Sepp Blatter ya yanke hukuncin sauka daga mukaminsa ne a wani jawabi da ya gabatar wa manema labarai a hedkwatar hukumar da ke Zurich na Suwazilan. kasa da mako daya bayan an sake zabar Blatter a matsayin shugaban Hukumar ne ya dauki wannan mataki.
Shugaban ya bukaci Hukumar ta gaggauta zaben sabon shugaban hukumar da zai maye gurbinsa. Sai dai Hukumar ta ce za ta gudanar da zaben sabon shugaban hukumar ne a tsakanin watan Disamba zuwa na Maris din 2016. Kenan Blatter zai cigaba da rike ragamar hukumar kafin a gudanar da sabon zaben.
Idan za a tuna, kimanin makwanni biyu ke nan da jami’an tsaron Amurka suka yi wa hedkwatar hukumar FIFA kawanya inda suka kama manyan jami’anta su kimanin 14 da ake zargi da laifin cin hanci da rashawa tun daga shekarar 1984 kawo yanzu.
Akwai zargin Afirka ta Kudu sai da tab a wadansu daga jami’an hukumar cin hanci kafin a ba ta damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 2010 sai dai tuni mahukuntan kasar suka karyata wannan batu.
Sepp Blatter dai ya shafe wa’adin mulki har sau hudu, na shekara hur-hudu a jere kuma an sake zabarsa a wa’adi karo na biyar a zaben da aka yi a makon jiya amma dambarwar cin hanci da rashawa a hukumar ta tilasta masa yin murabus a kasa da mako daya.
Kawo yanzu jami’an tsaro suna cigaba da gudanar da bincike don ci gaba da zakulo jami’an da ke da hannu wajen cin hanci da rashawa a hukumar.