Zargin cinye kudi: Kotu ta amince Hadiza Gabon da ‘masoyinta’ su yi sulhu

Jaruma Amal Umar ta bukaci kotu ta hana ’yan sanda kama ta.

Zargin cinye kudi: Kotu ta amince Hadiza Gabon da ‘masoyinta’ su yi sulhu

Hadiza Gabon

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Kaduna, ta dage sauraron karar da aka shigar da fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon zuwa ranar 15 ga Nuwamba, domin su samu damar sulhu a tsakaninsu.

Aminiya ta ruwaito yadda wani ma’aikacin gwamnati, mai suna Bala Musa ya shigar da karar jarumar bisa zargin cewa ya kashe mata kudi har Naira 396,000 da sunan suna soyayya, inda a cewarsa ta yi masa alkawarin za ta aure shi.

Jarumar ta musanta ikirarin, inda ta ce sam ba ta ma san shi ba.

A wata sabuwar kuma, jaruma Amal Umar ta bukaci kotu ta hana ’yan sanda kama ta.

Jarumar ta shiga cakwakiya ce bayan an zargin wani saurayinta mai suna Ramadan da cin kudin wani abokin kasuwancinsa.

An zargi saurayin jarumar ce da hallaka makudan kudi har Naira miliyan 40 da aka ba shi domin su yi kasuwanci.

Lauyan wanda yake karar saurayin na Amal, Barista Dan Sulaiman ya ce, lokacin da aka nemi kudi daga saurayin mai suna Ramadan ne sai ya bayyana cewa, ya saya wa budurwarsa Amal, motar Naira miliyan biyar.

“Ya kuma kama mata shago tare da zuba mata kayayyaki na Naira miliyan biyar don yin kasuwanci, kuma ya ba mahaifinta Naira miliyan uku.”

Sai dai jarumar ta nemi Babbar Kotun Jihar Kano da ke Miller Road ta hana ’yan sanda kama ta da kuma bincikar ta.

Lauyarta Barista Adama Usman, ta yi karar Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda mai Kula da Shiyya ta Daya, da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano da kuma dan sanda mai bincike a ofishin Shiyya ta Daya ne sakamakon zargin da saurayin ya yi mata na cin kudin wani abokin kasuwancinsa.

Aminiya ta gano cewa, bayan ’yan sanda sun samu wadannan bayanai, sai suka kwace motar Amal tare da ci gaba da bincikar ta kan wadancan kudade.

Alkalin Kotun, Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya sa ranar 16 ga Nuwamban nan, don ci gaba da sauraron karar tata.